An gudanar da kuri’ar raba gardama a Scotland

Fiye mutane miliyan hudu mazauna yankin Scotland ne suka kada kuri’arsu jiya (Alhamis) don bayyana ra’ayinsu kan ko za su ci gaba da kasancewa karkashin Birtaniya, ko kuma a’a.Kodayake, a shekaranjiya Laraba kuma rana ta karshe ta kamfe tsakanin bangarorin biyu, jagoran masu goyon bayan samun ‘yancin, kuma Ministan yankin Aled Salmond ya roki masu […]

An gudanar da kuri’ar raba gardama a Scotland
An gudanar da kuri’ar raba gardama a Scotland

Fiye mutane miliyan hudu mazauna yankin Scotland ne suka kada kuri’arsu jiya (Alhamis) don bayyana ra’ayinsu kan ko za su ci gaba da kasancewa karkashin Birtaniya, ko kuma a’a.
Kodayake, a shekaranjiya Laraba kuma rana ta karshe ta kamfe tsakanin bangarorin biyu, jagoran masu goyon bayan samun ‘yancin, kuma Ministan yankin Aled Salmond ya roki masu kada kuri’a kada su bari wannan damar ta samun kasa mai ‘yancin cin-gashin-kai ta wuce su a wannan karon. Inda ya ce, “zaben raba gardamar muhimmiyar dama ce a gare su”
Gabanin kada kuri’ar a jiya, ra’ayin shugabannin manyan jam’iyyun kasar wato Conserbatibe da Labour da kuma Liberal Democrat, ya zo daya kan batun, inda duka suka nuna rashin goyon bayan ballewar yankin daga Birtaniyar.
Hakazalika, gwamnatocin wasu kasashen nahiyar Turai da dama, ciki har da: Spain da Belgium da kuma Italiya, suma ba sa goyon bayan samun ’yancin yankin. Kodayake, hakan bai rasa nasaba da yadda hakan zai kara wa masu neman ballewa daga wadannan  kasashen kaimi. Misali a kasar Spain akwai yankin arewacin kasar, wato Cataloniya da ya dade yana fafutukar neman ’yancin kansa daga kasar. A kasar Belgium ma batun haka yake don akwai yankin Flander da shi ma yake neman ’yancin cin-gashin-kai.  Sai kuma ’yan awaren yankin arewacin kasar Italiya wato Northern League, wadanda suke neman ballewa don kafa kasar kansu, wadda suka wa lakabi da Padaniya.
kuri’un jin ra’ayoyin jama’a da aka gudanar a lokuta daban-daban har sau uku, kafin kuri’ar ta jiya a yankin Scotland, sun nuna cewa tazarar da ke tsakanin masu neman ballewa da kuma masu son yankin ya ci gaba da zama karkashin Birtaniya, ba ta da yawa sosai. Amma ana sa ran samun kammalallen sakamakon kuri’ar raba gardamar (yau) Juma’a.