An gudanar da sallah kan matsin rayuwa da tsaro a Jigawa

Talakawa na ci gaba da kokawa kan halin matsin rayuwa da ake tsaka da shi a Najeriya.

An gudanar da sallah kan matsin rayuwa da tsaro a Jigawa

Wata ƙungiya mai suna Sawaba Humanitarian Initiative ta jagoranci gudanar da taron addu’a don samun ƙarshen rashin tsaro da taɓarɓarewar tattalin arziki da suka jefa ’yan Najeriya cikin tsaya mai wuya.

An gudanar da addu’ar ne a Dutse, babban birnin Jihar Jigawa, yayin da duk ƙoƙarin da jami’an tsaro suka yi na daƙile masu shirya taron ya ci tura.

Ɗaruruwan mutane da suka halarci taron, sun nuna damuwarsu kan makomar ƙasar nan ganin yadda talauci, yunwa da cututtuka ke kashe mutane a kullum yayin da masu riƙe da madafun iko ko kuma masu mulki ba su nuna damuwa a kai ba.

Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala taron, shugaban ƙungiyar, Kwamared Umar Danjani Hadejia, ya ce al’amura a ƙasar nan na ƙara taɓarɓarewa ga talaka.

“Na kasa shawo kan hawayena bayan ganin yunwa na yi wa tsofaffi da mata da yara a ƙauyukan Jihar Jigawa illa.

“Babu wani shugaban siyasa mai tunani da zai yi barci cikin kwanciyar hankali bayan ya ga abin da na gani a ƙauyuka da dama,” in ji shi.

Danjani, ya ce ya damu matuƙa da irin wahalhalun da ya gani a waɗansu unguwanni, inda magidanta ke jinginar da kadarorinsu don cin abinci, yayin da wasu kuma ke kwashe kadarorin domin dawainiyar gidajensu.

A baya irin wannan hali ya sanya ƙungiyar ƙwadago ta Nijeriya (NLC), shiga yajin aiki don kira da shugabanni kan yadda kayan masarufi ke yin tashin gwauron zabi.

A jihohi da dama irin wannan yajin aiki da zanga-zanga ta gudana, wanda daga bisani Babban Bankin Najeriya (CBN), ya fara ɗaukar matakan daƙile tashin dala, wanda a cewar babban bankin dalar na da alaƙa da tashin kayayyaki.