An gudanar da taro kan cutar Ebola a Ghana
Ministocin Kiyon Lafiya 11 daga kasashen Afirka sun gudanar da taro a babban birnin kasar Ghana, Accra a wani mataki na ganin an dakile yaduwar cutar Ebola mai saurin kisa a yankunansu.A yanzu dai fiye da mutum 700 ne suka kamu da kwayar cutar kuma wasu fiye da 400 ne cutar ta yi ajalinsu yawancinsu […]

Ministocin Kiyon Lafiya 11 daga kasashen Afirka sun gudanar da taro a babban birnin kasar Ghana, Accra a wani mataki na ganin an dakile yaduwar cutar Ebola mai saurin kisa a yankunansu.
A yanzu dai fiye da mutum 700 ne suka kamu da kwayar cutar kuma wasu fiye da 400 ne cutar ta yi ajalinsu yawancinsu daga kasar Guinea inda annobar ta fara barkewa a watan Janairun da ya gabata. Daga nan ne kuma ta bulla kasar Liberiya da Sierra Leone masu makwabtaka da ita.
Ministocin sun fito ne daga kasashen Ibory Coast da Jamhuriyar Dimukradiyyar Kongo da Gambiya da Guinea da Mali da Senegal da Uganda da kasar Ghana mai masaukin baki da dai sauransu.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce akwai bukatar yakar kwayar cutar Ebola domin ganin ba ta ci gaba da yaduwa ba a yankin da ma duniya baki daya.
A ranar Talatar da ta gabata ne a wani mataki na yaki da cutar, Shugabar kasar Liberiya Ellen Johnson Sirleaf ta ce za a gurfanar da duk wanda aka kama a kasar da boye mutanen da ke dauke da kwayar cutar. Misis Sirleaf ta bayyana hakan ne ta wani gidan rediyon kasar: “Duk mahalukin da aka kama da laifin ajiye mai fama da cutar a gidaje ko a cocici maimakon kai shi asibiti, zai fuskanci fushin hukuma”, inji ta.