An gudanar da taron kungiyar daraktoci a Kano
kungiyar Daraktocin fina-finan Hausa ta kasa wacce aka fi sani da PROFDA ta yunkuro don inganta ayyukanta tare da neman hadin kan ’ya’yanta.Bayanin hakan ya fito daga bakin Jami’in Hulda da jama’a na kungiyar, Darakta Hassan Giggs a lokacin da kungiyar ta gudanar da babban taronta a Kano ranar Litinn.Darakta Giggs ya shaida wa Aminiya […]
kungiyar Daraktocin fina-finan Hausa ta kasa wacce aka fi sani da PROFDA ta yunkuro don inganta ayyukanta tare da neman hadin kan ’ya’yanta.
Bayanin hakan ya fito daga bakin Jami’in Hulda da jama’a na kungiyar, Darakta Hassan Giggs a lokacin da kungiyar ta gudanar da babban taronta a Kano ranar Litinn.
Darakta Giggs ya shaida wa Aminiya cewa sun gudanar da taron ne don samo bakin zaren wasu matsaloli da suka sha kanta.
“Kasancewar a yanzu daraktoci a wannan masana’anta muna tafiya babu wani tartibin tsari, ya sa kungiyarmu wacce aka kafa a 2011 ta ga dacewar gudanar da wanann taro, inda a zaman muka zabi shugabannin kungiyar don samun nasarar tafiyar da ita, sannan muka fitar da wasu tsare-tsare da dokoki don tabbatar da ingancin aikin kungiyar.
“A yanzu dai mun fara raba fom don tantance ’yan kungiyar, daga nan sai mu gudanar da aikin tantancewa, don sanin wadanda suka cancanta su gudanar da sana’ar tare da taimakon wadanda suke da rauni, don ganin an gudu tare an tsira tare “ Inji shi.
Ya ce kasancewar darakta shi ne kashin bayan fim, ma’ana kyawun fim ko akasinsa ya dogara ne a kansa, don haka akwai kalubale a kan darakta wajen ganin ya tsaya don ganin aikinsa ya inganta.
Giggs ya ce ’yan kungiyar za su amfana da sabuwar tafiyar, inda za a rika ba horo ta hanyar daukar nauyinsu zuwa kasashen waje ko kuma a gayyato masu bayar da horon daga kasar waje su zo su horar da ’ya’yanta a Najeriya.
Shugabannin da aka zaba don jan ragamar kungiyar sun hada da Mika’il Hassan a matsayin shugaba da kuma Aminu Saira mataimakin shugaba na daya da Bello M. Bello, mataimakin shugaba na biyu da Abdullahi Shehu, sakatare da mataimakinsa Sadik M. Mafia da kuma Falalu dorayi a matsayin Ma’aji da Muhamad Alfazazi a matsayin Mataimakin ma’aji.
Sauran shugabannin sun hada da Hassan Giggs a matsayin Jami’in Hulda da jama’a da kuma Hussaini Ali a matsayin mataimakinsa. Haka kuma akwai manajan shirye-shirye Mansur Sadik da kuma Edita Manir K.