An gudanar da wa’azi kan cika kwana 100 na gwamnatin Buhari
An gudanar da addu’o’i na musamman tare da wa’azi kan cikar Shugaban kasa Muhammadu Buhari kwana 100 a gadon mulki a Babban Masallacin kasa da ke Abuja.A wa’azin da ya gabatar wajen taron fitaccen malamin addinin Musuluncin nan kuma Babban Sakataren kungiyar Izala ta kasa Sheikh Kabir Haruna Gombe wanda ya yi wa’azi kan illar […]
An gudanar da addu’o’i na musamman tare da wa’azi kan cikar Shugaban kasa Muhammadu Buhari kwana 100 a gadon mulki a Babban Masallacin kasa da ke Abuja.
A wa’azin da ya gabatar wajen taron fitaccen malamin addinin Musuluncin nan kuma Babban Sakataren kungiyar Izala ta kasa Sheikh Kabir Haruna Gombe wanda ya yi wa’azi kan illar cin hanci da rashawa ya yi kira ga al’ummar Musulmi kan su yi aikin gaskiya da adalci, inda ya ce babu abin da ke yi wa kasa illa ya jefa ta a cikin mummunan hali illa rashin nagartaccen shugabanci da cin hanci da rashawa da sauransu.
Sheikh Kabiru Gombe ya ce shugabanci ba abin wasa ba ne, kuma ba kowa ake danka wa shugabanci ba, sai dai a zakulo mutum wanda aka san ya cancanta don a samu nasara.
Ya ce “A yanzu ’yan siyasa da malaman addini da talakawa da sarakuna da ’yan kasuwa da almajirai, kusan kashi saba’in na ’yan Najeriya sun yarda da cewa Allah Ya kawo sauye-sauye na alheri a cikin wadannan kwanaki dari na mulkin Muhammadu Buhari. Fargaba da dan Najeriya yake da ita ba mu tunanin za a kara wata shida a Najeriya tana nan.”
Shehin Malamin ya ce idan aka zagaya za a ga kowa jininsa ya dawo jikinsa, hankali ya kwanta, “Ba wai kwata-kwata matsalar ta kare ba ne, don ba ya yiwuwa cikin ’yan kwanaki a kawar da matsalar da aka yi shekaru ana yi, amma dai kowa ya san an dauki matakan da suka kamata, kuma ga nasarori nan Allh Yana ta kawowa, nan da dan lokaci komai zai zama tarihi,” inji shi.
Malamin ya kara da cewa, a shugabancin baya ya nemi Sheikh Abdullahi Bala Lau, suka rika bin sako-sakon Najeriya suna kira ga mutane su fahimci shugabancin Najeriya, ba wai matsalar addini ba ce matsalar ce ta ’yan Najeriya, sai sun hadu sun zabi mutumin da ya dace kowa zai samu moriya. “Idan ana maganar shugabanci, kamar likita ne idan ba ka da lafiya, ba damuwarka ba ne likitan da zai duba ka Musulmi ne ko ba Musulmi ba, kai dai kwararren likita da zai iya sanin abin da ke damunka shi ne damuwarka, haka maganar shugabanci take, sai an samu shugaba mai amana, sannan tafiyar za ta yi daidai. Sai ya bukaci Shugaban kasa ya nada wadanda suka cancata don su yi aiki da shi.
Sheikh Kabir Gombe ya yi kira ga mutane kan su sani cewa dukiyar haram ba ta rufa asiri, don Allah Ya isan talakawa ba ta faduwa a banza.