An gudanar da zaben majalisa a Libya 1
A shekaranjiya Laraba ne jama’ar kasar Libya suka je rumfunar zabe domin kada kuri’arsu a zaban ’yan majalisar kasar duk da rikicin da kasar take ciki. Wanda ya samo asali tun bayan hanbarar da gwamnatin Muammar Gaddafi a shekarar 2011.Mutane kusan miliyan daya da rabi ne suka kada kuri’arsu ga ’yan takara wadanda suka kai […]
A shekaranjiya Laraba ne jama’ar kasar Libya suka je rumfunar zabe domin kada kuri’arsu a zaban ’yan majalisar kasar duk da rikicin da kasar take ciki. Wanda ya samo asali tun bayan hanbarar da gwamnatin Muammar Gaddafi a shekarar 2011.
Mutane kusan miliyan daya da rabi ne suka kada kuri’arsu ga ’yan takara wadanda suka kai kimanin 1628 da ke fafatawa a kujerun majalisar kasar guda 200.
Wannan ne dai zaben ’yan majalisa karo na uku da aka gudanar tun bayan kawo karshen mulkin shugaba Muammar Gaddafi shekara uku da suka wuce.
Zaben na gudana ne a wani yanayi na rikici a kudancin kasar da kuma hare-haren da dakarun da ke karbar umarni daga Janar Khalifa Haftar suke kai wa. Wanda kuma suke samun goyon bayan dakarun sojin kasar Libya a yakin da janar din ke jagoranta a birnin Benghazi. Ko da yake a ranar zaben ba a samu tashin hankali ba a can. Amma hakan bai rasa nasaba da aiyana tsagaita wuta na kwana guda da Janar Khalifa ya ce zai yi.
Har ila yau, kafar yada labarai ta Aljazeera ta ruwaito cewa a babban birnin kasar,Tripoli zaben ya gudana lami lafiya. Ba tare da wani tashin hankali ba a baki dayan kewayan birnin.
An ware wa mata kujerun majalisa guda 30. A wani kokari na tabbatar da daidaito tsakanin su da takwarorinsu maza. A lokacin hada wannan rawoton, hukumomi ba su kai ga bayyana lokacin da za a fara samun sakamakon zaben ba tukuna.