An gudanar da zaben raba-gardama kan tsarin mulki a Masar
Al’ummar Masar sun kada kuri’a kan kundin tsarin mulkin kasar, a daidai lokacin da gwamnati ta yi gargadin daukar matakin kada-ta-kwana kan duk wani yunkuri na kawo cikas ga zaben na yini biyu.Ana shirya kundin ne domin maye gurbin tsarin mulkin da Shugaban kasar mai kishin Musulunci, Muhammad Morsi ya kaddamar kafin sojoji su hambarar […]
Al’ummar Masar sun kada kuri’a kan kundin tsarin mulkin kasar, a daidai lokacin da gwamnati ta yi gargadin daukar matakin kada-ta-kwana kan duk wani yunkuri na kawo cikas ga zaben na yini biyu.
Ana shirya kundin ne domin maye gurbin tsarin mulkin da Shugaban kasar mai kishin Musulunci, Muhammad Morsi ya kaddamar kafin sojoji su hambarar da mulkinsa a watan Yuli.
kungiyar ’Yan uwa Musulmi, (Ikhwanul Muslimina) da sojojin kasar suka haramta suka kuma kira da ta ’yar ta’adda ta nemi a kaurace wa kada kuri’ar.
Sabon tsarin mulkin dai ya haramta jam’iyyu masu akidar addini, kuma ya bunkasa hakkin mata, amma ya kara tabbatar da karfin sojoji a harkar mulkin Masar.
Sojojin suna bukatar samun rinjayen masu goyon bayan zaben kafin ya zama tsarin mulki ga kasar.
A rana ta farko ta zaben an kashe mutum biyar a fafatawar da ta gudana, inda aka kashe mutum daya a lokacin zanga-zangar adawa da zaben raba-gardamar a garin Bani Suyif da ke Kudancin Alkahira kamar yadda gwamnan yankin ya tabbatar wa gidan rediyon BBC.
Mutum uku kuma sun rasa rayukansu ne a fafatawa da jami’an tsaro a birnin Sohak, yayin da aka samu rahoton muuwar mutum daya a garin Nahiya da ke yankin Giza da ke gundumar Alkahira.
Kafin fara gudanar da zaben wani bam ya tashi a kusa da ginin wata kotu a gundumar Imbaba da ke Alkahira, sai dai ba a samu rahoton mutuwa a harin ba.
Kimanin sojoji dubu 160 da fiye da ’yan sanda dubu 200 ne aka tura sassan kasar domin sanya ido kan zaben.
Wani kakakin bangaren siyasa na Ikhwanu Mohammed Soudan, ya ce galibin jama’a sun kaurace wa zaben, “Wannan wani sako ne cewa ba mu yarda da wannan sabon iko ba,” inji shi.
Firayi Ministan riko Hazem Beblawi ya bayyana zaben da “Lokaci mafi muhimmanci” ga Masar.
Tsarin mulkin wanda wakilai 50 ciki har da na jam’iyyun Musulunci biyu suka rubuta ya tanadi zango shekara hudu sau biyu ga Shugaban kasa, kuma majalisa tana iya tsige shi. Sannan ya tabbatar da daidaito a tsakanin maza da mata, tare da haramta kafa jam’iyya kan addini ko kabila ko jinsi ko yankin kasa, yayin da sojoji za su ci gaba da nada ministan tsaro nan da shekara takwas.