An gurfanar da Amal kan zargin bai wa dan sanda cin hanci
An gurfanar da jarumar kan bayar da cin hanci domin hana binciken saurayinta.
An gurfanar da fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood, Amal Umar a gaban Kotun Majistare da ke Gyadi-Gyadi a Jihar Kano, kan zargin yunkurin bai wa wani jami’in dan sanda cin hanci.
Ana zargin jarumar da yunkurin bayar da cin hancin Naira 250,000 ga wani dan sanda, mai suna ASP Salisu Bujama, da ke rundunar ’yan sandan, shiyya ta daya da ke Kano.
- Majalisa ta amince da ƙudirin yi wa Alƙalai ƙarin albashi
- Tinubu ya haramta wa ministocinsa fita ƙetare
A cewar mai gabatar da karar, Amal na yunkurin bayar da cin hancin ne domin hana binciken ’yan sanda kan zargin saurayinta da almundahanar kudi.
Rundunar ta bayyana haka ne a wani taron manema labarai da kakakin na shiyya ta daya da ke Kano, CSP Bashir Muhammad ya gabatar a ranar Laraba.
Ya kara da cewa, “Wata jaruma ’yar wasan Hausa wadda aka fi sani da Amal Umar mai shekara 24, an gurfanar da ita a gaban kotu domin yunkurin bayar da cin hanci da ta yi ga ASP Salisu Bujama wanda yake bincike kan wani batu na damfara ta Naira miliyan 40 da saurayinta ya yi wa wani Alhaji Yusuf Adamu.”
Wannan na zuwa ne, bayan da wani Yusuf Adamu ta hannun lauyansa ya shigar da korafi ga mataimakin Babban Sufeton Umar Mohammad Sanda, inda yake zargin saurayin jarumar da yin sama da fadi da kudin da ya kai Naira miliyan 40 da sunan kasuwanci.
Ƙorafin da aka shigar ya sa ’yan sanda gudanar da bincike, inda suka gano cewa saurayin jarumar ya tura mata Naira miliyan 13 zuwa asusun ajiyar bankinta.
A cewar kakakin ’yan sandan, CSP Bashir Muhammed, an gayyaci jarumar domin amsa tambayoyi daga bisani kuma aka bayar da belinta, sai dai an hana ta fita daga wata mota da ake zargin saurayin nata ne ya siya.
Jarumar ta tabbatar cewa kudin da ke cikin asusunta mallakin saurayinta ne duk da ta yi ikirarin cewa Naira miliyan takwas kawai ya tura mata.
Bayan da aka bayar da belinta ne kuma ta garzaya babbar kotu domin neman a dakatar da ’yan sanda daga binciken da suke a kanta.
Kotun ta hana ci gaba da binciken da ’yan sanda ke yi mata, abin da ya bai wa Amal dama ta yunkurin ba da toshiyar baki ga dan sandan da ke bincike a kan lamarin, ASP Salisu Bujama.
Sai dai dan sandan ya ki karbar cin hancin, lamarin da kai ga gurfanar da ita a gaban kotun Majistare a ranar Laraba.
Laifin da ake zargin jarumar ta aikata ya saba wa sashe na 118 na dokar final kod, wadda ta haramta bai wa jami’in dan sanda cin hanci.