An gurfanar da barawon zinaren N8.9m a kotu
Wani mutum mai shekara 48 ya gurfana a gaban kuliya bisa zargin sace wani sako mai dauke da zinare da lu’ulu’u a ciki.
Wani mutum mai shekara 48 ya gurfana a gaban kuliya bisa zargin sace wani sako mai dauke da zinare da lu’ulu’u a ciki.
’Yar sanda mai gabatar da kara, ASP Rita Moma, ta shaida wa alkali cewa darajar zinare da lu’ulu’un da ake zargin mutumin ya sace ta kai Naira miliyan 8.9.
- Ambaliya ta tafi da gawa 500 daga makabarta a Neja
- DAGA LARABA: Tashin Hankalin Da Samari Ke Ciki Amma Suke Boyewa
- 2023: Ina da koshin lafiyar da zan jagoranci Najeriya —Tinubu
Momah ta gurfanar da wanda ake zargin ne bisa tuhumar aikata sata da kuma hada baki, a gaban Babbar Kotun Majistare da ke zamanta a Yaba, Jihar Legas.
Ta shaida wa kotun cewa mutumin ya yi awon gaba da sakon da aka aika wa wani mai suna Temitope Badiru, da aka sanya zinare da lu’ulu’un a ciki.
Ta ce wanda ake zargin yi gaban kansa da zinare da lu’ulu’un Mista Temitope ne a ranar 7 ga watan Yuli, 2022.
A cewarta hakan laifi ne karkashin Sashe na 287 da kuma 411 na Dokar Hukunta Manyan Laifuka ta Jihar Legas ta 2015.
Sai dai wanda ake tuhumar ya musanta zargin.
Alkalin kotun ta ba da belin sa a kan Naira miliyan daya.
Ta kuma shardanta masa kawo mutum biyu da za su tsaya masa, wadanda kowannensu zai ajiye Naira miliyan daya.
Daga nan ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 5 ga watan Oktoba, 2022.