An gurfanar da dagaci kan rigimar fili

An gurfanar da Dagacin Shekar Maidaki da ke Jihar Kano Malam Badamasi Abdulkadir a gaban Kotun Lardi ta Shari’ar Musulunci da ke Nomansland da ke birnin Kano bisa zarginsa da laifin hadin baki da cinye wa wani talakansa fili. Ana zargin Malam Badamasi Abdulkadir da laifin hadin baki da wata mace mai suna Zainab Aminu […]

An gurfanar da dagaci kan rigimar fili
An gurfanar da dagaci kan rigimar fili

An gurfanar da Dagacin Shekar Maidaki da ke Jihar Kano Malam Badamasi Abdulkadir a gaban Kotun Lardi ta Shari’ar Musulunci da ke Nomansland da ke birnin Kano bisa zarginsa da laifin hadin baki da cinye wa wani talakansa fili.

Ana zargin Malam Badamasi Abdulkadir da laifin hadin baki da wata mace mai suna Zainab Aminu danja inda suka cinye wa wani mai suna Aminu Yusuf filinsa.
Aminiya ta gano cewa daya matar da ake zargi wato Zainab ta gudu lamarin da ya sa ba ta bayyana a gaban kotun ba. Sai dai Dagacin ya musanta laifin da ake zarginsa da shi.
Alkalin Kotun Mai shari’a Faruk Ahmad ya dage sauraren shari’ar zuwa mako biyu tare da bayar da belin Dagacin da sharadin Dagacin ya kawo matar da suka yi laifin tare a zaman kotun na gaba.