An gurfanar da dalibi a gaban kotu kan zargin boye budurwa
An gurfanar da wani dalibin Jami’ar Jihar Gombe mai suna Gambo M. Daniel a gaban Babbar Kotun Majistare ta Shida da ke Gombe bisa zarginsa da laifin boye wata budurwa mai suna Tabitha Kone, dalibar Kwalejin Ilimin Fasaha ta Tarayya da ke garin Gombe.Ana zargin Gambo Daniel ne da laifin boye Tabitha a dakinsa tun […]
An gurfanar da wani dalibin Jami’ar Jihar Gombe mai suna Gambo M. Daniel a gaban Babbar Kotun Majistare ta Shida da ke Gombe bisa zarginsa da laifin boye wata budurwa mai suna Tabitha Kone, dalibar Kwalejin Ilimin Fasaha ta Tarayya da ke garin Gombe.
Ana zargin Gambo Daniel ne da laifin boye Tabitha a dakinsa tun cikin watan Afrilun har zuwa ranar 23 ga watan Yulin bana ba tare da sanin iyayenta ba inda ya mayar da ita tamkar matarsa.
dan sanda mai gabatar da karar, Saje Bako Shekari, ya shaida wa kotun cewa aikata hakan laifi ne da ya saba wa sashi na 272 na kundin laifuffuka da hukuncinsu (Penal Code).
Da kotun ta juya wajen Gambo dangane da zargin da ake yi masa sai ya musanta laifin, daga nan sai dan sanda mai gabatar da karar ya shaida wa kotun cewar suna da shaidu kuma a shirye suke su gabatar da su.
Sai dai iyayen Tabitha Kone da na Gambo Daniel da suka halarci zaman kotun sun ce ba sa bukatar ci gaba da shari’ar, inda suka ce iyayen Gambo sun same su har gida sun roke su a kan su janye, kuma sun duba zaman tare sun janye karar.
Lauyan wanda ake tuhuma Barista S.A. Sati, ya shaida wa kotun cewa iyayen yaran duk sun daidaita don haka yake rokon kotu da ta sallami karar.
Sai alkalin kotun Mai shari’a Nana A’isha Bappah, ta sallami karar kamar yadda suka nema, sai dai ta yi musu gargadi a matsayinsu na dalibai cewa kada hakan ta sake faruwa, maimakon haka su mayar da hankali kan karatunsu.