An gurfanar da dan siyasar Kano a kotu kan barazanar dukan malamin addini
Malamin ya ce Anas ya yi barazanar lakada masa duka
Kotun Majistare mai lamba 60 da ke zamanta a Nomansland a Jihar Kano ta gurfanar da dan siyasar nan, Anas Abba Dala gabanta bisa zargin yin barazanar duka ga Malam Lawal Abubakar Limamin Masallachin Juma’a na Triumph da ke Kano.
Tun da farko mai gabatar da kara Barista Lamido Abba Sorondinki ya shaida wa kotun cewa tun a ranar 29 ga watan Satumba malamin ya kai karar dan siyasar ga ofishin ’yan sanda da ke Bompai.
- Rashin kyan hanyoyin Najeriya ne ya sa za mu sayi motoci masu tsada – Majalisar Dattawa
- An ci tarar Kano Pillars miliyan daya kan kutsen magoya baya cikin filin wasa
Malam Lawal ya bayyana cewa a ranar 15 ga watan 9 wanda ake kara ya yi barazana tare da shan alwashin a duk lokacin da ya hadu da shi, sai ya sa magoya bayan wata akidar siyasa sun masa dukan tsiya.
Sai dai wanda ake zargin ya musanta laifin da ake zargin sa da shi.
Lauyan wanda ake zargin, Barista Hassan Tanko Kyaure, ya nemi kotun ta bayar da belin wanda ake zargin inda kuma a take kotun ta amince.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Tijjani Garba Minjibir, ya sanya ranar 3 ga watan Nuwamban 2023 don ci gaba da sauraren shari’ar.
Sai dai wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa a yanzu haka ana kokarin yin sulhu a tsakanin bangarorin biyu.