An gurfanar da Fayose a kotu a Legas

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati EFCC ta gurfanar da tsohon Gwamnan jihar  Ekiti Ayo Fayose a gaban babbar kotun tarayya a jihar Legas. An dai gurfanar da Fayose ne a yau Litinin kan tuhume-tuhume 11 ciki har da laifukan cin hanci da rashawa da sauransu. Alkalin kotun Mojisola Olatiregun ne […]

An gurfanar da Fayose a kotu a Legas

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati EFCC ta gurfanar da tsohon Gwamnan jihar  Ekiti Ayo Fayose a gaban babbar kotun tarayya a jihar Legas.

An dai gurfanar da Fayose ne a yau Litinin kan tuhume-tuhume 11 ciki har da laifukan cin hanci da rashawa da sauransu.

Alkalin kotun Mojisola Olatiregun ne ya jagoranci shari’ar

Sai dai tsohon gwamnan ya musanta duka wadannan tuhume-tuhumen.