An gurfanar da jami’in gwamnatin Goodluck a kotu
A ranar Talata ne aka gurfanar da tsohon Mashawarcin Shugaban Kasa Goodluck Jonathan a kan Harkokin Tsaro Kanar Sambo Dasuki (mai ritaya) a gaban kotu a Abuja bisa zarginsa da mallakar makamai ba tare da lasisi baKanar Sambo Dasuki, wanda aka gurfanar da shi a gaban kotun kan laifi daya na mallakar makamai ba tare […]
A ranar Talata ne aka gurfanar da tsohon Mashawarcin Shugaban Kasa Goodluck Jonathan a kan Harkokin Tsaro Kanar Sambo Dasuki (mai ritaya) a gaban kotu a Abuja bisa zarginsa da mallakar makamai ba tare da lasisi ba
Kanar Sambo Dasuki, wanda aka gurfanar da shi a gaban kotun kan laifi daya na mallakar makamai ba tare da lasisi, Daraktan Shigar da kararraki na kasa Mohammed Diri ni ya shirya tuhumar.
Laifin a cewar daraktan ya saba wa sashi na 27 (1) (a) (i) na dokar mallakar makamai mai lamba CAP F28 LFN, 2004.
Sai dai Dasuki ya ki amincewa da zargin, inda nan take lauyoyinsa Joseph Daudu (SAN) da Ahmed Raji (SAN) suka nemi a bayar da belinsa.
A lokacin da yanke hukunci kan bukatar belin Alkalin Kotun Mai shari’a Adeniyi Ademola ya umarci wanda ake tuhumar ya mika fasfo dinsa na tafiye-tafiye zuwa kasashen duniya da fasfo dinsa na diplomasiyya ga magatakardan kotun.
Hukumar Tsaron kasa (DSS) ta ce ta samu manyan bindigogi kirar Tabor guda biyar a mamayen da ta kai gidansa na Asokoro da ke Abuja a watan Yuli, sai wata bindiga kirar Uzi mai lamba 60244 da makunsan harsasai guda 20 da fakitin harsashi na Ma’aikatar Tsaro samfurin AP9 mai girman milimita tara tare da lambar Luger 033373.
Sauran kayayyakin da ta yi zargin samu tare da Dasuki sun hada da karamin makunshin harsashi da ke dauke da harsasai 16 da babban makunshin harsashi makare da harsasai.
Mai gabatar da karar ya hada da shaidun da aka gano da takaitaccen bayanin tuhumar da jerin shaidu da jerin kayan da aka samu da rantsuwar abubuwan da aka binciko da bayanin wanda ake tuhuma da na shaidun da za a gabatar.
Bayan cika sharuddan belin, an tuka Dasuki a wata bakar marsandi samfurin E399 mai lambar Abuja, GW 155 NU. Dasuki ya samu rakiyar tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Attahiru Bafarawa da tsohon Minista a Ma’aikatar Kudi, Bashir Yuguda da tsohon mai tsara yaki da ta’addanci a ofishinsa kuma dan takarar Gwamnan Jihar Kebbi a karkashin Jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata Manjo Janar Bello Sarkin Yaki.
An dage sauraren shari’ar zuwa 26 da 27 ga Oktoba mai zuwa.
A wani labarin kuma Hukumar Yaki da Cin-hanci da Rashawa ta kasa (ICPC), ta fara bincike a kan wasu tsofaffin gwamnoni kasar nan hudu da ake zargi da almundahana da dukiyar gwamnati, sakamakon wasu takardun korafi da aka rubuta a kansu.
Tsofaffin gwamnonin kamar yadda gidan rediyon BBC ya ruwaito, sun hada da tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da takwaransa na Jihar Ribas Mista Rotimi Amaechi da na Enugu, Sulliban Chime da kuma Ibrahim Shema na Jihar Katsina.
Tuni dai hukumar ta tashi tawagogi hudu zuwa jihohin domin su binciki kundin ajiye bayanai na jihohin don tabbatar da gaskiyar zargin da ake wa gwamnonin.
Hukumomin yaki da cin hanci da rashawa dai sun zage dantse wajen gurfanar da duk wanda ake zargi da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya haye karagar mulki.