An gurfanar da ma’aikacin asibiti da ya kashe majinyata 100 a Jamus

Wani tsohon ma’aikacin asibiti mai suna Niels Högel ya amsa laifin kisan majinyata 100, wanda hakan ya sa ya zama daya daga cikin wadanda suka shahara a kashe mutane a jere da adadin su ya kai guda 100. Masu bincike sun ce, Niels Högel na baiwa majinyata kwayoyin da zasu yi masu illa lokacin da […]

An gurfanar da ma’aikacin asibiti da ya kashe majinyata 100 a Jamus

Wani tsohon ma’aikacin asibiti mai suna Niels Högel ya amsa laifin kisan majinyata 100, wanda hakan ya sa ya zama daya daga cikin wadanda suka shahara a kashe mutane a jere da adadin su ya kai guda 100.

Masu bincike sun ce, Niels Högel na baiwa majinyata kwayoyin da zasu yi masu illa lokacin da yake lura dasu a asibitoci biyu a Arewacin Jamus.

Manufar Niels Högel shi ne, ya birge abokan aikinsa ta hanyar samun saukin jinyar marasa lafiya a asibitin a kulawar shi.

Högel dan shekara 41 wanda bada dade wa ba ake tuhumarsa da rasuwar mutum shida a kulawarsa. A yanzu kuwa Högel ya ce, ya kashe majinyata 36 a lardin Oldenburg jihar Lower Sadony da ke Jamus da kuma yin ajalin majinyata 64 a garin Delmenhorst daga shekarar 1999 zuwa 2005

Alkalin kotun Oldenburg ya ce idan har kotun ta kammala binciken Högel zai dauki hukuncin ajalin rasuwar duk mutanen da ake zarginsa ko kuma kusan hakan.

An dai fara sauraren shari’ar ne da shirun mintuna don yin addu’a ga wadanda suka rasa rayukansu. An dai dau shekaru ana gwajin musabbabin rasuwar wasu mutanen da ake zargin rasuwarsu a sanadiyyar zuba masu guba.

 

Dalilin da ba zan bai wa Gwamnatin Tinubu shawara ba — Sarki Sanusi

Hamas da Isra’ila sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

HOTUNA: Yadda aka yi bikin tunawa da mazan jiya a faɗin Nijeriya

Sanusi zama daram kuma Sarki ɗaya tilo a Kano — Falana