An gurfanar da masoyan da suka kai wa malami hari a Kano

Dukkaninsu sun musanta tuhume-tuhumen da ake musu, wanda hakan ya sa aka ɗage shari’ar.

An gurfanar da masoyan da suka kai wa malami hari a Kano

Wata ɗaliba daga Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano, mai suna Khadija Hassan Chiranchi, da kuma saurayinta Khalid Hussain wanda aka fi sani da Baffa, sun gurfana a gaban kotun Shari’ar Musulunci kan zargin kai wa malami hari.

Rahotanni sun bayyana cewa, Khadija ta gayyato saurayinta Khalid zuwa ofishin malamin, Aliyu Hamza Abdullahi, wanda ta ce yana zame mata matsala a karatunta.

A lokacin ne saurayin ya zaro adda ya sari malamin a kai.

Dukkaninsu sun gurfana a kotu kan tuhume-tuhumen da suka haɗa da, haɗa baki, aikata daba, kutse da cin zarafi.

Sun musanta zargin da ake musu, inda suka ce kotun ba ta da hurumin sauraron shari’ar.

Duk da haka, alƙalin kotun ya bayar da umarnin a tsare su a gidan yari har zuwa ranar 27 ga Fabrairu, 2025, don sake gurfanar da su.

Sai dai kuma, an zargi saurayin da mallakar makami mai hatsari, wanda ya amince da laifin.

Wanda a nan ne kotun ta ce tana da hurumin sauraron wannan ɓangaren na zargin, wanda ya sa aka ɗage shari’ar zuwa wannan rana domin ci gaba da sauraron ta.