An gurfanar da matasa 57 da ake zargi da luwadi a legas

Hukumar ’Yan sandan Jihar Legas ta gurfanar wadansu matasa 57 a gaban Kotun Majestare da ke Yaba bisa zarginsu da laifin aikata luwadi.  A ranar Alhamis din makon jiya ne sashin binciken manyan laifuffuka na Hukumar ’Yan sandan (SCIID) da ke  Unguwar Panti, Yaba, ya gabatar da wadanda ake zargin. Cyril Ajufor, jami’in da ya […]

An gurfanar da matasa 57 da ake zargi da luwadi a legas
An gurfanar da matasa 57 da ake zargi da luwadi a legas

Hukumar ’Yan sandan Jihar Legas ta gurfanar wadansu matasa 57 a gaban Kotun Majestare da ke Yaba bisa zarginsu da laifin aikata luwadi. 

A ranar Alhamis din makon jiya ne sashin binciken manyan laifuffuka na Hukumar ’Yan sandan (SCIID) da ke  Unguwar Panti, Yaba, ya gabatar da wadanda ake zargin.

Cyril Ajufor, jami’in da ya gabatar da wadanda ake zargin a gaban kotun ya shaida wa Majistare Kikilemo Ayeye cewa ’yan sandan sun kama wadanda ake zargin ne a wani otel da ke Unguwar Ebgeda a ranar 26 ga watan jiya da misalin karfe 2 na dare, sakamakon bayanan sirri da suka samu cewa matasan na aikata luwadi, wanda laifi ne da ya saba wa kundin dokokin Jihar Legas.

Wadanda ake zargin sun musanta aikata laifuffukan da ake tuhumarsu, inda Majistaren ta ba da belinsu a kan Naira dubu 200 kowannensu, ta kuma dage sauraron karar zuwa 10 ga watan nan da muke ciki.

Tun da farko Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Legas Edigal Imohimi ya gabatar wa manema labarai wadanda ake zargin inda ya ce ’yan kungiyar asiri ne da ke rantsar da sababbin mambobinsu ta hanyar yin luwadi. Ya ce ’yan sanda sun far musu ne a wani otal din da suka shirya yin aika-aikar a tsakiyar dare, inda suka kama matasa 57 yayin da ragowar suka tsere. Ya ce an same su da kayayyakin maye da suka hada da benelin da wiwi, wadanda suke sanyawa a ruwan shisha.

Sai dai matasan sun musanta zargin aikata luwadi, inda suka  ce sun taru a otel din ne domin bukukuwan rawa da kade-kade.