An gurfanar da Matashi saboda cizon Budurwarsa a Mama
Wani matashi dan shekara 25, Chibuike Njokwu da ake zargi da gantsara wa budurwarsa cizo a nononta na hagu, a ranar Laraba ya gurfana gaban wata Babbar Kotu Majistire da ke zamanta a birnin Ado-Ekiti. Jami’in dan sandan da ya gabatarwa da kotun Njokwu wanda mazauni ne a Unguwar Surule, yana tuhumarsa da laifin cin […]
Wani matashi dan shekara 25, Chibuike Njokwu da ake zargi da gantsara wa budurwarsa cizo a nononta na hagu, a ranar Laraba ya gurfana gaban wata Babbar Kotu Majistire da ke zamanta a birnin Ado-Ekiti.
Jami’in dan sandan da ya gabatarwa da kotun Njokwu wanda mazauni ne a Unguwar Surule, yana tuhumarsa da laifin cin zarafi da kuma yi wa budurwarsa mummunan rauni.
Sufeta Oriyomi Akinwale ya shaida wa kotun cewa matashin da ake kara ya aikata laifin ne yayin da wata ’yar hatsaniya ta shiga tsakaninsa da budurwarsa da misalin karfe 7.00 na safiyar ranar 24 ga watan Dasimba a birnin Ado-Ekiti.
Akinwale ya ce wanda ake tuhumar ya gantsara wa budurwarsa mai suna Ifunanya Okonkwo cizo a mamanta na hagu, wanda hakan ya janyo mata rauni mai muni.
Ya ce wannan laifi yana cin karo da sashe na 335 cikin dokokin miyagun laifuka na Jihar Ekiti, inda ya roki kotun ta dage sauraron karar domin ya samu damar tattaro hujjoji da zai gabatar mata.
Lauyan wanda ake kara, Mista Emmanuel Sumonu, ya roki kotun da ta bayar da belin matashin yayin da ya gabatar mata dalilai na bukatarsa kamar yadda shari’a ta tanada.
Alkaliya Adefumike Anoma ta amsa bukatar hakan inda ta bayar da belin wanda ake kara a kan naira dubu hamsin tare da neman ya gabatar da mutum daya da zai tsaya masa.
Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN ya ruwaito cewa an dage sauraron karar zuwa ranar 26 ga watan Janairun 2021.