An gurfanar da mutum 10 a gaban kotu kan kisan Fulani 27 a Jos

Ana zarginsu ne da kisan Fulani matafiya 27 a Jos.

An gurfanar da mutum 10 a gaban kotu kan kisan Fulani 27 a Jos

Gwarwakin wasu daga cikin matafiyan da aka kashe a Jos

A Jihar Filato, an gurfanar da mutum 10 a gaban Babbar Kotun Jihar bisa zargi kisan wasu Fulani matafiya a Unguwar Rukuba da ke Jos.

Ana dai zargin mutanen ne da hannu a kisan wasu Fulani matafiya kimanin 27 ranar 14 ga watan Agusta a unguwar Rukuba da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa, lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa Jihar Ondo daga Bauchi.

’Yan sanda ne dai suka gurfanar da mutanen ta hannun jami’a mai shigar da kara, Muleng Alex.

’Yar sandan dai ta shaida wa kotun cewa  wadanda ake zargin, Mathew Daniel da Juarbe Zamani da Dapar Sunday da Bernard Francis da Daniel Bulus da Solomon Dung da Yakubu John da Stephen Ishaku da Yohanna Marshal da Dakwak Sunday, sun yi amfani da muggan makamai da suka hada da wukake da duwatsu wajen aikata laifin.

Kazalika, ta kuma shaida wa kotun cewa hukuncin laifin nasu shi ne kisan kai, kamar yadda sassa na 188 da na 189 na kundin manyan laifuka suka tanada.

Muleng ta kuma fada wa kotun cewa daya daga cikin wadanda ake zargin, Solomon Dung, shekarunsa 17 ne kawai, kuma yaro ne da bai kamata a aike da shi kurkuku ba.

Sai dai dukkan wadanda ake zargin sun musanta aikata laifin.

Lauya mai kare wadanda ake zargin, Barista Yakubu Bawa ya roki kotun da ta tsare mutum taran kawai a kurkuku, amma ta ajiye Solomon a gidan horon yara saboda karancin shekarunsa.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Arum Ashom ya amince da bukatar sannan ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 13 ga watan Oktoba mai zuwa.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50