An gurfanar da mutum 41 kan haƙar ma’adanai a Oyo

Wannan laifi ne wanda ya saba wa dokar haƙar ma’adanai da ke karkashin sashe na 516 a Kundin Dokokin Nijeriya.

An gurfanar da mutum 41 kan haƙar ma’adanai a Oyo

(Hoto: us.fotolia.com)

An gurfanar da wasu mutum 41 kan zargin haƙar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a Jihar Oyo.

Aminiya ta ruwaito cewa, an gurfanar da mutanen a gaban mai shari’a U.N Agomoh wanda ya jagoranci zaman kotun da aka gudanar ranar Alhamis a Ibadan, babban birnin jihar.

Mai gabatar da ƙara, Mista Michael Ojeah, ya shaida wa kotun cewa, an kama ababen zargin ne a ranar 25 ga watan Janairun da ya gabata.

Mista Ojeah ya bayyana cewa an kama mutanen ne suna tsakar haƙar ma’adanai ba tare da izini ba a ƙauyen Onipanu da ke Ibadan.

Ya ƙara da cewa, an samu ababen zargin da wani dutsen zinare da suka haƙo mai nauyin giram 24.96 wanda darajarsa ta kai kimamin naira miliyan ɗaya da dubu ɗari biyu har da ɗoriya.

Kazalika, ya ce wannan laifi ne wanda ya saba wa dokar haƙar ma’adanai da ke karkashin sashe na 516 a Kundin Dokokin Nijeriya na 2004.

Sufeton ’yan sanda Awosanmi Abiola, wanda ya jagoranci jami’an tsaro da suka kama mutanen, ya gabatar wa kotun bayanan da suka yi kafin a kawo su kotu.

Duka mutanen 41 da aka gurfanar gaban kotun sun amsa laifin da ake tuhumarsu da aikatawa.

Bayan sauraron bayanan ne mai shari’a Agomoh ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 11 ga watan Maris.

Zaɓen Edo: Duk wanda ya kaɗa ƙuri’a ya koma gida ya zauna — ’Yan sanda

Hotunan yadda Zaɓen Gwamnan Edo ke gudana

An buƙaci mazauna Benuwe su yi ƙaura saboda fargabar ambaliyar ruwa

Abubuwan da ya kamata ku sani game da Zaɓen Edo