An gurfanar da mutum 97 wadanda ake zargi a rikicin Kaduna
Hukumar ‘yan sandan jihar ta gurfanar da mutum 97 wadanda ake zargi da hannu a rikicin jihar Kaduna. Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ahmad Abdurrahman ya ce, hukumar ‘yan sandan ta mika wadanda ake zargin a kotun Majistiri ta 1 da ke layin, Ibrahim Taiwo a Kaduna. Kwamishinan ya kara da cewa, an sake kama wasu […]
Hukumar ‘yan sandan jihar ta gurfanar da mutum 97 wadanda ake zargi da hannu a rikicin jihar Kaduna.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ahmad Abdurrahman ya ce, hukumar ‘yan sandan ta mika wadanda ake zargin a kotun Majistiri ta 1 da ke layin, Ibrahim Taiwo a Kaduna.
Kwamishinan ya kara da cewa, an sake kama wasu mutum 27 akan laifuka da dama, da suka hada da: fashi da makami, garkuwa da mutane, sata da aikata fyade.