An gurfanar da Saminu Turaki a gaban kotu kan almundahanar Naira biliyan hudu

Wata Babbar Kotun Shari’a da ke Dutse a Jihar Jigawa a karkashin Mai shari’a Ubale Ahmed Taura ta karbi karar da gwamnatin jihar ta shigar tana zargin tsohon Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Saminu Turaki da tsohon Shugaban Majalisar Jihar Alhaji Mustapha Malam Makama Kiyawa da Bashir Turaki dan uwan tsohon Gwamnan da kuma kamfanin Gehel […]

An gurfanar da Saminu Turaki a gaban kotu kan almundahanar Naira biliyan hudu
An gurfanar da Saminu Turaki a gaban kotu kan almundahanar Naira biliyan hudu

Wata Babbar Kotun Shari’a da ke Dutse a Jihar Jigawa a karkashin Mai shari’a Ubale Ahmed Taura ta karbi karar da gwamnatin jihar ta shigar tana zargin tsohon Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Saminu Turaki da tsohon Shugaban Majalisar Jihar Alhaji Mustapha Malam Makama Kiyawa da Bashir Turaki dan uwan tsohon Gwamnan da kuma kamfanin Gehel Nigeria Limited da ake zargin mallakar tsohon Gwamnan nan ne, da aikata wasu laifuffuka shida da suka shafi almundahana.
Takardar karar da Aminiya ta ci karo da ita mai lamba JDU/23/2014  ta nuna za a fara sauraren karar ce a ranar 12/6/2014.
Kotun ta aike wa wadanda ake karar da takardar sammaci su bayyana a gabanta don amsa tuhumar yin sama-da-fadi da dukiyar talakawan Jihar Jigawa da kuma zamba cikin aminci da mallakar kamfani ba bisa ka’ida ba, wanda hakan ya saba wa sashi na 97 na dokar Final Kod da sashi na 109 na dokar Jihar Jigawa, inda ake zarginsu da almundahana da kudaden kananan hukumomin jihar da suke amsa daga Asusun Tarayya kimanin Naira biliyan hudu.
Takardar ta kara da cewa ana zargin tsohon Gwamnan da yin jabun takardar da ta ba majalisar jihar damar amincewa ya ciwo bashin naira biliyan hudu daga bankin Garaunty Trus Bank wanda hakan laifi ne a karkashin sashi na 97 da 109 cikin baka na dokar Jihar Jigawa.
Takardar ta zargi Alhaji Mustapha Makama Kiyawa da umartar wani Rabi’u Ibrahim ya rubuta wa a jami’an gwamnatin jihar takarda yana bukatar su amince gwamnatin ta ciwo bashin Naira biliyan hudu daga bankin na Garaunty Trust ba tare da amincewar majalisar jihar, kuma yin hakan laifi ne da ya saba wa sashi na 85 da 109 na dokar Jihar Jigawa na 1998. Shi kuwa dan uwan tsohon Gwamnan ana zarginsa ne da amfani da takardar biza ta jabu da aka yi amfani da ita wajen fitar da wasu makudan kudi ta hanyar sa hannun a fita da makudan kudi mallakar jihar daga bankin Garaunty kuma hakan ya saba wa sashi na 364 na dokar jihar.
Ana zargin Bashir Turaki da zambatar Aminu Idris kan zai amshi wancan takardun biza mallakar Idris Ibrahim zai kai shi Makka kuma da su ne aka samu damar aikata wasu daga cikin miyagun laifuffukan da ake tuhumarsu da shi a halin yanzu.