An gurfanar da shi kan bata sunan Sanata Rufa’i Hanga

Kotun ta amince da bayar da belinsa kan Naira dubu dari biyu

An gurfanar da shi kan bata sunan Sanata Rufa’i Hanga

Sanata Rufai Sani Hanga

Babbar Kotun Majistare mai lamba 19 da ke zamanta a unguwar Nomanslan ta Jihar Kano, ta gurfanar da mai magana da yawun dan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya na Jam’iyyar APC a Zaben 2023, A.A Zaura, wato Ahmad Dahiru Maiwuddadu bisa zarginsa da bata wa Sanatan Kano ta Tsakiya, Rufa’i Sani Hanga suna.

Mai gabatar da kara, Barista Fatima Ado Ahmad ta shaida wa kotun cewa ana tuhumar Maiwuddadu da laifin bata suna da tayar da hankali.

A kunshin karar da ta gabatar, Barista Fatima ta shaida wa kotun cewa Maiwuddadu ya yi wa Sanata Rufai kazafin cewa mashayi ne kuma yana bata kudin al’ummar Jihar Kano ta Tsakiya wajen shaye-shaye.

Sai dai bayan karanto masa takardar karar, Maiwuddadu ya musanta dukkanin laifukan da ake zarginsa da aikatawa.

Lauyansa ya roki kotun ta bayar da belinsa, lamarin da mai gabatar da kara ba ta kalubalanta ba.

Kotun dai ta amince ta bayar da belinsa kan Naira dubu dari biyu da mutane biyu da za su tsaya masa wadanda kowannensu ya mallaki dukiyar da ta kai Naira dubu dari biyu.

Haka kuma, kotun ta ce dole ne wadanda za su tsaya masa daya daga cikinsu ya kasance ma’aikacin gwamnati ne mai matakin albashi na goma sha biyu da kuma Mai unguwa ko Dagaci.

Kotun ta kuma sanya ranar 29 ga watan Fabarairu 2024 domin ci gaba da shari’ar.

HOTUNA: Ɗaurin auren ’yar Kwankwaso ya haɗa Atiku, Obasanjo, Kashim Shettima da manyan ’yan siyasa a Kano

HOTUNA: An soma kaɗa ƙuri’a a Zaɓen Ondo

Mai hannu ɗaya da ke sana’ar faskare

Dole talauci ya yi katutu a Arewa!