An gurfanar da shi kan cizon mace a mama

A ranar Litinin ne jami’an rundunar ’yan sandan Jihar Lagas suka gurfanar da wani magidanci mai shekara 35, mai suna Uche Afokaigbo a gaban Kotun Majistare ta Itire bisa zarginsa da cizon wata mace a mama.Wanda aka zargin yana zaune ne a gida mai lamba 20, Titin Enoma, Ago-Palace Way a yankin Ago Okota, Legas, […]

An gurfanar da shi kan cizon mace a mama
An gurfanar da shi kan cizon mace a mama

A ranar Litinin ne jami’an rundunar ’yan sandan Jihar Lagas suka gurfanar da wani magidanci mai shekara 35, mai suna Uche Afokaigbo a gaban Kotun Majistare ta Itire bisa zarginsa da cizon wata mace a mama.
Wanda aka zargin yana zaune ne a gida mai lamba 20, Titin Enoma, Ago-Palace Way a yankin Ago Okota, Legas, kuma ana tuhumarsa ne da laifi daya na jawo rauni a gaban alkalin kotun Majistare Misis A. O. Gbajumo.
dan sanda mai gabatar da kara Sufeto Olukunle Shonibare ya shaida wa kotun cewa, wanda ake zargin ya ciji wata mai suna Kemi Oluwaja wadda makwabciyarsa ce a mamanta a ranar 12 ga Mayun bana.
Sufeto Shonibare ya bayyanana cewa, fada ya barke a tsakanin matar wanda ake zargi da mai karar kan wani abin girki wanda ya jawo wanda ake zargin ya sanya hannu, kuma ya ce, bayan Afokaigbo ya ciji mai kara a mama, ya kuma sace abin girkin nata.
Mai gabatar da karar ya shaida wa kotun cewa, laifin ya saba wa sashi na 171 na dokokin manyan laifuffuka na Jihar Legas na shekarar 2011.
Wanda ake zargin ya ki amsa laifinsa, inda alkalin kotun ta bayar da belinsa kan Naira dubu 100 da mutum biyu masu tsaya masa kuma ta dage fara sauraron shari’ar Litinin mai zuwa 23 ga Yunin nan.