An gurfanar da su a kotu kan zargin makwabcinsu da maita

Wasu mutum uku da ke kauyen Kugaru a karamar Hukumar Karu ta Jihar Nassarawa sun gurfana a gaban wata Babbar Kotun Jihar da ke garin Mararaba bisa zargin yi wa wani makwabcinsu zargin maita tare da barazanar kashe shi. Mutanen  dan’auta da danladi Kada da Lawal Salisu sun bayyana a gaban kotun ne a ranar […]

An gurfanar da su a kotu kan zargin makwabcinsu da maita
An gurfanar da su a kotu kan zargin makwabcinsu da maita

Wasu mutum uku da ke kauyen Kugaru a karamar Hukumar Karu ta Jihar Nassarawa sun gurfana a gaban wata Babbar Kotun Jihar da ke garin Mararaba bisa zargin yi wa wani makwabcinsu zargin maita tare da barazanar kashe shi.
Mutanen  dan’auta da danladi Kada da Lawal Salisu sun bayyana a gaban kotun ne a ranar Litinin da ta gabata sakamakon karar da makwabcinsu ya shigar kai-tsaye.
Mai karar ya sanar da kotun cewa, bayan komawarsa kauyensu a ranar 9 ga Agusta daga kasuwar wani gari, ya samu labarin cewa mutane sun kai kararsa wajen Dagajin garinsu kuma a sakamakon hakan Dagacin ya bukaci ya bayyana a fadar kashegai tare da su. Ya ce da ya je fadar ya tarar da gungun jama’a da suka kai dari, tare da mutanen suna dakon zuwansa.
Ya ce “Na je wurin Dagacin, kuma a gaban Dagacin mutane ukun da jama’a suka bi su zuwa cikin fadar, suka nufo kaina suna cewa sai sun kashe banza, sannan suka ce ina tsoratar da wanda ake zargi na farko da dansa a lokacin da suke barci.”
Ya ce sai dai wasu suka kubutar da shi a lokacin kuma sakamakon barazanar da suke yi masa ya kaurace wa kauyensu tun daga wancan lokaci.
Bayan karanta karar, jami’in kotu da ya karanta a madadinsa ya ce abubuwan da ake zargin mutanen da aikatawa da ya hada da gama kai wajen aikata laifi da batanci da barazana ga rayuwa, laifuffuka ne da suka saba wa dokoki na 97 da 392 da kuma 397 na Final Kod.
Da Alkalin Kotun Mai shari’a bincent W. Gwahemba ya waiwayi wadanda ake karar sun musunta laifuffukan sannan suka bukaci a ba da belinsu.
Kotun ta ba da belinsu a kan Naira dubu 50 kowannensu tare da wadanda za su tsaya musu daga yankin da kotun ke da hurumi, sannan Alkalin ya dage zaman shari’ar zuwa ranar 14 ga watan Satumba.