An gurfanar da tsofaffi kan laifin fyade
A Larabar da ta gabata ce aka gurfanar da wadansu tsofaffi su biyu a gaban babbar kotun Majestiri ta 6 da ke Unguwar GRA a Katsina.Malam Haladu Abdu dan shekara 65 da kuma Malam Ashiru Musa dan shekara 64, dukkansu mazauna Sabuwar Unguwa da ke cikin babban birnin Jihar Katsina, an gurfanar das u ne […]
A Larabar da ta gabata ce aka gurfanar da wadansu tsofaffi su biyu a gaban babbar kotun Majestiri ta 6 da ke Unguwar GRA a Katsina.
Malam Haladu Abdu dan shekara 65 da kuma Malam Ashiru Musa dan shekara 64, dukkansu mazauna Sabuwar Unguwa da ke cikin babban birnin Jihar Katsina, an gurfanar das u ne bisa zargin yi wa wata yarinya mai suna Yusra Shu’aibu ’yar shekara 11 fyade.
Da yake gabatar da su gaban mai shari’a, Nafisa L. Bagiwa, dan sanda mai gabatar da kara Sufeto Hashimu Musa ya shaida wa kotun cewa, mahaifin yarinyar ne ya kai wa ofishin ’yan sanda na Sabon Gari koken lalata masa diya ta hanyar yi mata fyadd ta hanyar hade kai tare da yin amfani da karfi don yin lalata da ita a cikin wani shago da ke Sabuwar Unguwar; wanda hakan ya janyo yi mata rauni a matancinta.
dan sandan mai gabatar da kara ya ce laifin da ake tuhumar wadannan dattawa da aikatawa ya saba wa sashe na 97 da 283 na dokar kundin laifuffukan Finalkod. Sai dai mai shari’a ta shaida wa wadanda ake tuhumar cewa, an kawo su kotun ne domin ambata shari’ar amma kotunta ba ta da hurimin yin wannan shari’a. Ta kuma ba da ummurnin a kai su gidan yari har zuwa ranar da za a fara sauraren karar tasu.