An gurfanar da tsohon alƙali a kotu kan dukan matar aure a Zariya

An zargi tsohon alƙali da dukan matar aure wadda makauniya ce suke zaune a gidan haya ɗaya.

An gurfanar da tsohon alƙali a kotu kan dukan matar aure a Zariya

(Getty Images)

An gurfanar da tsohon aƙalin kotun shari’ar Musulunci, Mahmoud Shehu, a gaban kotun majistare da ke Tudun Wada Zariya, kan laifin cin zarafin wata matar aure Sadiya Mohammed wadda makauniya ce.

Ɗan sanda mai gabatar da ƙara, Sufeto Adamu Abubakar, ya shaida wa kotun cewa a ranar 6 ga watan Satumba, mijin matar mai suna Garba Adda’u, ya kai rahoto ofishin ’yan sanda da ke Tudun Wada Zariya, cewar Mahmoud Shehu ya rufe ƙofar gidan da suke haya tare da bin matarsa Sadiya har ɗaki tare da dukanta.

Ya bayyana cewar wanda ake zargin ya doki matar da sandar lema tare dukan yara biyu da ke zaune da ita, wanda ta kai ga kai su asibiti.

Ya ce laifin ya saɓa wa sashe na 327 da 237 da kuma 239 na kundin penal kod na 2017.

Lauyan wanda ake ƙara, SM Abubakar, ya nemi kotun ta ba da belin wanda ake tuhuma, kasancewarsa tsohon alƙali.

Sai dai ɗan sanda mai gabatar da ƙara ya ƙi amincewa da buƙatar da lauyan.

Ya ce ba zai yarda a bayar sa belin wanda ake tuhuma ba kasancewar gida ɗaya suka zaune da wadda lamarin ya shafa.

Alƙalin kotun, Lukman Sidi, ya bayar da belin wanda ake ƙara, Mahmoud Shehu, kan kuɗi Naira dubu 50 tare da gabatar da mutum ɗaya wanda zai tsaya masa.

Har wa yau, kotun ta buƙaci ya ajiye fasfo ɗinsa da kuma cikakken adireshinsa.

Kotun ta ce idan ya gaza cika wannan sharaɗi za ta sa a tasa ƙeyarsa zuwa gidan gyara hali har zuwa ranar 8 ga watan Oktoba 2024, domin ci gaba da sauraron ƙarar.

Kotun ta kuma umarci dukkanin ɓangarorin biyu da su zauna lafiya da junansu kuma duk wanda ya saɓa umarnin kotun zai fuskanci hukunci.

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta