An gurfanar da tsohon fira ministan Pakistan kan zargin rashawa

Gwamnatin kasar Pakistan ta gurfanar da tsohon Fira Minista Imran Khan bisa zargin sayar da kyaututtukan gwamnati ba bisa ka’ida ba

An gurfanar da tsohon fira ministan Pakistan kan zargin rashawa

Gwamnatin kasar Pakistan ta gurfanar da tsohon Fira Minista Imran Khan bisa zargin sayar da kyaututtukan gwamnati ba bisa ka’ida ba.

An gurfanar da Mista Imran Khan ne a ranar Laraba bayan daruruwan jami’an tsaro sun tsare shi a ranar Talata bisa zargin almundahana, zargin da ya musanta.

Tsarewar da aka yi masa dai ta harifar da tarzoma a kasar, inda jami’an tsaro suka tsare daruruwan magoya bayansa.

A baya zargin sayar kyaututtukan ya sa hukumar zaben kasar (ECP) ta haramta wa tsohon fira ministan tsayawa takara na shekara biyar kan zargin rashawa.

Hukumar ta haramta masa takara ne bisa samun sa da laifin yi wa gwamnati karya game da kyaututtukan da shugabannin kasashen waje suka yi mishi a zamanin mulkinsa.

Dambarwar siyasar ta kunno kai ne bayan wasu shari’o’i da tsohon shugaban da aka sauke a watan Afrilu tare da jam’iyyarsa ta PTI suke fuskanta.

Tarzoma a sasssan Pakistan

Tun bayan sanar da matakin a ranar Juma’a magoya bayan Imran Khan da PTI suka yi ta farfasa motoci bayan sun bar hedikwatar hukumar; ’yan sanda sun tsare wani mai gadin jam’iyyar bayan ya yi harbi a kasa.

A wani bidiyo a ranar Juma’a, Imran Khan, ya yi kira ga magoya bayansa su kwantar da hankalinsu, yana cewa zai jagornaci tattakin magoya bayansa a Islamad kafin karshen watan Oktoba da muke ciki.

Ya ce, “Ina rokon ku da ku dakatar da zanga-zangar saboda tana cutar da mutane, sannan ba na kaunar ganin kasarmu ta shiga cikin matsala.”

Imran Khan zai garzaya kotu

Ya bayyana cewa zai kalubalanci hukuncin hukumar a kotu, yana mai zargin ta da hada baki da miyagu a gwamnati.

“Matukar ina raye, zan ci gaba da yakar miyagun da ke cikin gwamnati, ciki har da shugaban hukumar zabe.”

Shari’ar zabe kan dauki tsawon lokaci a kotunan Pakistan, wanda kungiyoyin kare hakki ke zargin amfani da su wajen tadiye ’yan adawa.

Sai dai kuma matakin da ECP ta dauka kan Imran Khan na da alaka ne da bukatar zababbun su bayyana duk kadarorinsu.