An gurfanar da tsohon Shugaban karamar Hukumar Akko a kotu kan zargin zamba cikin aminci
A ranar Talata 2 ga watan Yulin nan ne wani mai suna Alhaji Muhammad Baba, ya yi karar tsohon shugaban karamar Hukumar Akko Alhaji Baba Sarkin Fulani a gaban Kotun Yanki ta unguwar Pantami a garin Gombe, kan zarginsa da yi masa zamba cikin aminci.Alhaji Muhammad Baba, ya shaida wa kotun cewa yana karar Alhaji […]
A ranar Talata 2 ga watan Yulin nan ne wani mai suna Alhaji Muhammad Baba, ya yi karar tsohon shugaban karamar Hukumar Akko Alhaji Baba Sarkin Fulani a gaban Kotun Yanki ta unguwar Pantami a garin Gombe, kan zarginsa da yi masa zamba cikin aminci.
Alhaji Muhammad Baba, ya shaida wa kotun cewa yana karar Alhaji Baba Sarkin Fulani a gaban kotun ne saboda ya karbi kudinsa Naira dubu 524 a kan zai sama masa kujerar aikin Hajji, amma bai sama masa kujerar ba kuma bai ba shi kudin ba, sannan babu magana mai dadi don haka ne yake neman kotu ta karba masa kudinsa.
Alhaji Baba Sarkin Fulani, bai halarci zaman kotu ba, duk da cewa an aike masa da sammaci, ganin haka ne sai kotun ta aike a je a kamo shi saboda raina amsa kiran kotu da ya yi.
Ana cikin haka sai wani abokin Baba Sarkin Fulani, ya zo gaban kotun ya ba da hakuri kuma ya ce za a kawo kudin cikin mako biyu, inda ya ce mai karar da wanda ake kara abokan juna ne.
Mai karar ya amince da rokon don haka sai Alkalin kotun Alhaji Sambo Yero, ya dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar Talata 16 ga Yuli.
A wani labarin kuma Babbar Kotun ta Biyu ta Jihar Gombe ta daure wadansu mutum biyu da suka hada da Kabiru Ardo Buba da Modibbo Usman da suke da zaune a garin Kunuwal a karamar Hukumar Yamaltu Deba, shekara biyar-biyar hade da horo da aikin karfi ba tare da zabin biyan tara ba, sannan kuma da wani hukunci na daurin shekara daya ko biyan tarar Naira dubu talatin- talatin kowannensu, sakamakon samunsu da laifin kisan kai, yayin da ta sallami wanda ake tuhuma na uku Babayo Lamido (dan Madami) wanda kotun ta ce ba ta same shi da laifi ba.
A ranar 28 ga watan Disambar shekara ta 2010 ne aka gurfanar da mutanen uku ana tuhumarsu da kashe wani mutum mai suna Alhaji Umaru Bose, lokacin da ake gudanar da zaben wakilan Jam’iyyar PDP na Kunuwal wanda aikata hakan laifi ne da ya saba wa sashi na 97 (1) da sashi na 221 na kundin laifuffuka da hukuncinsu.
An tuhumi Kabir Ardo Buba da soke Alhaji Umaru Bose da wuka a gefen cikinsa inda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa.
Bayan da kotu ta kammala sauraron shaidu Alkalin Kotun Mai shari’a Sa’adu Muhammad, ya ce
Kabiru Ardo da Modibbo Usman, kotun ta same su da laifi na jawo rauni wanda ya saba wa doka ta 247 na Final Kod, laifin Modibbo Usman, shi ne a lokacin da Alhaji Umaru Bose, yake gudu don kada Kabiru Ardo, ya cim masa sai ya sanya masa kafa ya fadi har Kabiru Ardo ya zo ya sokes hi da wuka.