An gurfanar da wadanda ake zargi da kashe amaryar kwana 12

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta gurfanar da mutanen da ake zargi da kisan amaryar da aka kashe kwanakin baya a Unguwar Jaen da ke Kano a gaban Kotun Majistare ta 6 da ke Sakatariyar Audu Bako.Mutanen da ake zargi sun hada da Rabi’u Abdulkadir da AbdulZahir wadanda binciken ’yan sandan ya gano cewa sun […]

An gurfanar da wadanda ake zargi da kashe amaryar kwana 12
An gurfanar da wadanda ake zargi da kashe amaryar kwana 12

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta gurfanar da mutanen da ake zargi da kisan amaryar da aka kashe kwanakin baya a Unguwar Jaen da ke Kano a gaban Kotun Majistare ta 6 da ke Sakatariyar Audu Bako.
Mutanen da ake zargi sun hada da Rabi’u Abdulkadir da AbdulZahir wadanda binciken ’yan sandan ya gano cewa sun je gidan amaryar a ranar da aka kashe ta.
Mutanen su musanta zargin da ake yi musu, kuma lauyan gwamnati Barista dalhatu Usman ya ce laifuffuka ne uku da suka hada da kisa da fyade da hadin baki wajen aikata laifi. Haka kuma laifuka ne da suka saba wa sashi na 221 da 283 da 97.
Alkalin Kotun Mai shari’a Abba Kabara ya bayar da umarnin a tsare wadanda ake zargin a kurkuku tare da dage shari’ar zuwa ranar 28 ga Satumba.   
Idan za a iya tunawa a kwanakin baya wasu da ba a san ko su wane ne ba sun kashe amarya A’isha Isah Fagge a gidanta da ke Unguwar Jaen kwana 12 da aurenta