An gutsure kunnenta wajen tiyatar gyaran hanci
Wata mata a kasar China mai suna Misis Zhao mai shekara 31 da aka yi wa tiyatar sauya hanci a asibitin garin Chengdu ta yi matukar kaduwa bayan ta gano an gutsure mata kunne ba tare da saninta ba. Misis Zhao wanda aka yi wa tiyatar a asibitin Angel Wing a Chengdu a ranar 1 […]
Wata mata a kasar China mai suna Misis Zhao mai shekara 31 da aka yi wa tiyatar sauya hanci a asibitin garin Chengdu ta yi matukar kaduwa bayan ta gano an gutsure mata kunne ba tare da saninta ba.
Misis Zhao wanda aka yi wa tiyatar a asibitin Angel Wing a Chengdu a ranar 1 ga Satumban da ya gabata, wannan ne karo na biyu a shekara biyar da aka yi mata tiyatar, kuma wannan ne karo na farko da aka gutsure mata kunnen.
- Kifi mai rai ya makale a makogwaron masunci
- Yadda Zulum ya halarci jana’izar manoma 43 da aka yi wa yankan Rago
Zhao ta bayyana wa wata kafar labarai ta kasar China cewa ta yaba tiyatar kuma ta ji dadin aikin da aka yi mata.
Amma bayan kwana hudu sai ta kalli madubi ta fahimci cewa, akwai wani bangare da aka cire a jikin kunnenta na dama.
Daga waje zuwa ciki duk an cire wani bangare na kunnen duk da yake ba wanda ya fada mata.
Misis Zhao ta fusata inda ta tunkari likitocin asibitin game da yadda aka sauya halittarta.
Hakan ya sa ta sanya aka rubuta takardar yarjejeniya game da tiyatar da aka yi mata na gyaran hanci da za ta iya amfani da ita.
Zhao ta bayyana wa kafar labarai ta China mai suna The Paper cewa, ta tuntunbi kwararrun likitocin tiyata, sannan suka tabbatar da cewa za a iya cire wani bangaren kunne a yi amfani da shi wajen yin tiyatar hanci.
Mai Magana da Yawun asibitin, Angel Wing ya ce cire wani bangaren da aka yi wajen yin amfani da shi a hanci ka iya rage girman kunne.
Yanzu dai haka Zhao ta shigar da kara tana neman a biya ta kudi kan rashin biyan bukata sannan a mayar mata da kunnenta yadda yake.
Ta ce takan ji kunci idan ta kalli kunnenta, saboda wani bangare na iya cire wa gaba daya.
Rikicin Zhao da asibitin Chengdu ya janyo zazzafar gardama, wadda sai da ’yan sanda suka shiga tsakaninsu kuma kawo yanzu ba a kammala sasantawa a tsakaninsu ba.