An haife ni babu mahaifa da farji – Joanna
Wata matashiya ’yar kasar Girka Joanna Giannouli, ’yar shekara 27 ta koka da cutar da ke damunta, wadda a Likitanci ake kira da “Rokitansky syndrome,” al’amarin da ke nuni da cewa ba ta da al’aura da jijiyoyin da ke kulla alaka da mahaifa, har ta kai ga ba ta yin jinin al’ada, ballantana ta iya […]
Wata matashiya ’yar kasar Girka Joanna Giannouli, ’yar shekara 27 ta koka da cutar da ke damunta, wadda a Likitanci ake kira da “Rokitansky syndrome,” al’amarin da ke nuni da cewa ba ta da al’aura da jijiyoyin da ke kulla alaka da mahaifa, har ta kai ga ba ta yin jinin al’ada, ballantana ta iya tarawa da namiji.
Da take bayyana wa BBC yadda Likitan fida ya fitar mata da farji, lokacin da aka gano cewa babu mahaifa da jijiyoyin da ke hadewa da buda al’aura a jikinta.
Irin wannan cutar an kiyasta cewa, akalla mace guda a cikin dubu biyar na fama da ita, kuma suna fahimtar matsalar ne da zarar sun ki fara jinin al’ada a lokacin da suke tashen balaga.
Sabon farjin da likitoci suka yi mini ya yi kankanta, don haka nake jin zafi a lokacin jima’i, shi ya sa suka fadada shi.
Duk da cewa cikin farjin ba ya budewa sosai, matan da ke fama da wannan matsalar, nonon su na girma, gashin gaban su na fitowa.
Da take bayanin irin halin da ta shiga na kaka-ni-ka-yi, saboda wannan matsalar, al’amarin da ya hada da cewa ba za ta iya haihuwar ’ya’ya ba. Ta kuma yi bayanin yadda aka yi mata aiki, da tallafin da ta samu daga ’yan uwa da masoya, cewa su suka taimaka mata ta shawo kan matsalar.
Mahaifiyarta ta taba kai ta wurin likitoci tun tana ’yar shekara 14, amma sai bayan shekara biyu aka dauki hoton sassan jikinta, al’amarin da ya tabbatar tana fama da cutar Rokitansky.
An haife ni babu mahaifa da farji
– Joanna