An haifi bakwaini da jela mai tsawon sentimita 12

An haife shi da bakuwar jelar bayan gwaje-gwaje sun nuna ba shi da wata matsala.

An haifi bakwaini da jela mai tsawon sentimita 12

Wata mata ta haifi bakwaini mai jela da tsawonta ya kai sentimita 12 a garin Fortaleza da ke kasar Brazil.

An haife shi da jelar da ba a saba ganin irinta ba a kan duwawunsa na hagu ne bayan hoto da sauran gwaje-gwajen da aka yi na cikinsa sun nuna yana cikin koshin lafiya kuma ba ya tare da wata matsala.

Daga kasar jelar tasa mai tsawon sentimita 12 kuma akwai wani curin tsoka kamar da kwallo.

Shi dai wannan bakwaini an haife shi ne a asibitin yara na Albert Sabin da ke Fortaleza bayan mako 35 da daukar cikinsa.

Likitoci sun bayyana cewa mutum na 40 ke nan da aka samu da irin wannan halitta a tarihi.

A cewarsu, halittar dan Adam na da jela a lokacin da yake cikin mahaifa, amma daga baya jelar tana komawa jikinsa kafin a haife shi.

Sun kara da cewa babu gurunguntsi ko kashi a cikin kashin dake da jelar, kitse ne da tantani ne kawai a cikinsa.

Bayan gwaje-gwaje, likitoci sun gano cewa jelar da ke jikin bakwainin ba ta hade da lakarsa ba, saboda haka suka yi masa tiyata suka cire ta.

Sai dai babu wanni tabbacin ko yanke jalar ta shafi lafiyarsa, kuma yanan nan yana warkewa cikin koshin lafiya.

Bayan kammala aikin tiyatar cire jelar, likitoci sun gudanar da bincike a kan kwallon da ke kasanta, inda daga gano cewa zallar tantani ne kawai a cikinsa.