An haifi dan tsako da kafa hudu a Zariya
A ranar Litinin din makon nan wata kaza ta kyankyashe dan tsako da kafa hudu a gidan sanyi da ke layin Mangorori Tudun Jukun Zariya, a Jihar Kaduna. Mai wannan kaza, Lubabatu Musa ta yi wa wakilin mu bayani tarihin kazar kamar haka, inda ta ce,” ita dai wannan kaza an haifetane haka, kuma wannan […]
A ranar Litinin din makon nan wata kaza ta kyankyashe dan tsako da kafa hudu a gidan sanyi da ke layin Mangorori Tudun Jukun Zariya, a Jihar Kaduna. Mai wannan kaza, Lubabatu Musa ta yi wa wakilin mu bayani tarihin kazar kamar haka, inda ta ce,” ita dai wannan kaza an haifetane haka, kuma wannan ne kyankyasarta ta farko, kuma ta yi kwai biyar ne sai ta kyankyashe biyu, ta yi bara gurbin uku, sai wannan mai kafa hudun tare da dan uwan kyankyasar sa. Yana cin abinci, sai dai kuma ba inda ya kamata ya yi bahaya yake yi ba, shi wajen bahayar shi a tsakiyar cikin sa yake yi, ba kamar na sauran kaji ba. Ka ji yadda aka kyankyashe shi.