An haifi jarirai sama da 30 a sansanin ’yan gudun hijira ɗaya a Benuwe
Abin farin ciki, ba a sami rahoton mutuwar jariri ko ɗaya ba a tsawon watanni takwas.
Sama da jarirai 30 ne aka haifa a cikin watanni takwas a sansanin ‘yan gudun hijira ɗaya da ke ƙaramar hukumar Makurdi ta jihar Benuwe.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, sansanin ‘yan gudun hijira na NEPA Quarters da ke kusa da Bankin Arewa da ke birnin Makurdi ne ya sanar da haihuwar jariran da aka yi a tsakanin watan Fabrairun bana zuwa 31 ga Oktoba, 2024.
- Ruftawar gini ta laƙume rayukan mutum 10 a Ibadan
- An ƙara mafi karancin albashin Kaduna zuwa N72,000
Manajar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (Benuwe-SEMA) ta sansanin ‘yan gudun hijira na NEPA Quarters, Emmanuella Chagu, ce ta bayyana hakan a ranar Alhamis a lokacin da ake mayar da ‘yan gudun hijirar zuwa wani sabon matsuguni da aka gina a unguwar Mbayiongo a Ƙaramar Hukumar Makurdi.
Chagu ta ce, “An haifi jarirai 30 ne a tsakanin watan Fabrairun bana zuwa yau (31 ga Oktoba).
“Abin farin ciki, ba a sami rahoton mutuwar jariri ko ɗaya ba a wannan sansanin a tsawon wannan lokacin tun lokacin da aka tura ni sansanin NEPA Quarters.”
Ta bayyana cewa ana mayar da ‘yan gudun hijirar NEPA Quarters zuwa matsugunansu na asali bisa tsarin gwamnatin jihar Benuwe na tsugunar da duk mutanen da suka rasa matsugunansu a jihar.
Manajan sansanin ta ƙara da cewa sauya matsugunan ya ƙunshi mutane 835 da suka haɗa da magidanta 171 da suka zauna a sansanin tsawon shekaru da dama.
Chagu ta ce, farkon ƙidayar mutanen sansanin kaɗai ya kai 7,000 wanda ya ƙunshi magidanta 4,000, kafin adadinsu ya ragu bayan hijira zuwa wasu jihohin ƙasar nan domin neman dogarau da kai.