An haifi jariri da azzakari uku

A karon farko a tarihin aikin likitanci, an samu jaririn da aka haifa da azzakari uku

An haifi jariri da azzakari uku

A karon farko a tarihin aikin likitanci, an samu jaririn da aka haifa da azzakari uku.

Kafar yada labarai ta thenationonlineng.net ta fahimci cewa, likitocin na ikirarin wannan shi ne karon farko da suka taba ganin wanda aka haifa mai irin wannan halittar.

Shi dai wannan jaririn an haife shi ne da mafitsara uku wanda ake kiran haka da suna ‘Triphallia’ a likitance, watanni uku da suka wuce a garin Duhok da ke kasar Iraki.

Likitocin sun ce iyayen jaririn da aka haifa da mafitsarar uku sun gano hakan ne bayan samun shi dauke da loba biyu a jikinsa. A yayin da likitocin suke duba jikin jaririn sai suka yi mamakin yadda aka haife shi da halittar mafitsara uku a jikinsa.

A gwajin da aka yi wa tsawon azzakarin ukun, daya ya kai tsawon sentimita 2, daya kuma sentimita 1; amma daya ne kawai yake da kan azzakari kuma yake aiki kamar yadda ya kamata.

Daga nan sai likitocin suka yi tiyata wajen cire sauran biyun da aka haife shi da su.

Shugaban likitocin da suka yi tiyatar, Dakta Shakir Saleem Jabali ya wallafa rahoto game da abin mamakin da suka gani a mujallar International Journal of Surgery Case Reports:

“Haihuwar mutum da mafitsara uku mai suna Triphallia abu ne da har yau ba a taba wallafa shi a tarihi ba.

“Irin wannan tiyatar tana iya kasancewa mai wahala, saboda ba a cika samun masu irin wannan halittar ba. Yin hakan na bukatar shawarwarin kwararru da hadin gwiwa wajen yin aikin.”

Rabon da a samu jaririn da aka haifa da azzakari biyu —wanda masana suka ce a cikin yara maza miliyan shida za a iya samun guda a cikinsu— tun a shekarar1609, wanda wani likitan kasar Switzerland mai suna Johannes Jacob Wecker ya gano a jikin wata gawa.

Lakurawa sun kashe ma’aikatan kamfanin Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya