An haifi jariri da idanu uku a Kano

Fiye da makonni biyu da suka wuce aka haifi wani jariri a garin Rano ta Jihar Kano, wanda aka same shi da ido guda uku a maimakon biyu da aka saba samun kowane bil’adama da shi. Aminiya ta tatatuna da mahaifiyar jaririn mai suna Sajida Ashiru, ’yar kimanin shekaru 24 da haihuwa, inda ta bayyana […]

An haifi jariri da idanu uku a Kano
An haifi jariri da idanu uku a Kano

Fiye da makonni biyu da suka wuce aka haifi wani jariri a garin Rano ta Jihar Kano, wanda aka same shi da ido guda uku a maimakon biyu da aka saba samun kowane bil’adama da shi. Aminiya ta tatatuna da mahaifiyar jaririn mai suna Sajida Ashiru, ’yar kimanin shekaru 24 da haihuwa, inda ta bayyana cewa tunda lokacin da aka haifi jaririn suka gano cewa akwai wani kullutu a gefen idonsa na hagu, da suka zurfafa bincike sai suka gano ashe ido ne. 

“Da aka haife shi muka ga wani kullutu a gefen idonsa na hagu da farko mun dauka ciwo ne, sai da muka bincika sanann muka gano cewa wani idon ne daban. Ganin hakan ya sa muka kai shi asibitin Rano, inda su kuma suka turo mu nan asibitin” Inji nmahaifiyar jaririn.
Mahaifiyar jaririn ta bayyana wa Aminiya cewa ba ta samu wani bambanci tsakanin goyon ciki da kuma haihuwar jaririn da na sauran yayyensa\guda uku ba. Haka kuma ta bayyana cewa idan har likitoci suka yanke shawarar cire idon jaririn, to su a matsayinsu na iyyen yaron ba su da ja akan hakan.
A yanzu haka dai jaririn yana kwance a Asibitin kwararau na Murtala Muhamamd, inda kuma yake cike da koshin lafiya kamar yadda likitoci suka bayyana.
Dokta Hadi Bala Yahya, shi ne Shuagaban Sashen kula da lafiyar Idanu na Asibitin kwararu na Murtaal Muhamamad, ya shaida wa Aminiya cewa, a tarihin bangaren idanu ba a taba samun labarin faruwar hakan ba.
“lokacin da aka kawo jaririn mun gudanar da gwaje-gwaje daban-daban don gano shin ido ne ko kuwa, a nan muka gano cewa ido ne, wanda yake da komai na idanu da suka hada da bakin da farin da kuma gashin ido da murfi da sauransu. Da muka yi gwaji kuma mun gano cewa idon lafiyarsa lau yana gani. A tarihi an sha samun inda aka haifi mutun da ido daya, amma irin wannan ba a taba samu ba, sai dai ko idan an haifa ba a kai asibiti ba har jaririn ya mutu ko wani abu makamancin hakan” Inji shi.
Game da shirin da asibiti yake yi wajen tunkarar idon, Dokta Hadi ya bayyana cewa suna nan suna gudanar da bincike, wanda sakamakon binciken ne zai tabbatar da makomar idanun yaron, wato ko za a cire idon na ukun ko kuma za a bar shi.
“Akwai binciken da muke gudanarwa a yanzu game da makomar idon na ukun, idan muka gano cewa halitatrsa wacce ke kai gani zuwa kwakwalwa tana hade da sauran biyun, ta yadda idan aka taba shi zai shafi lafiyar wadancan idanun, to ba za mu iya yi masa aiki ba, sai dai a bar shi da idanunsa guda ukun. Idan muka gano ba a tare suke ba, to za mu yi masa aiki a cire. Idan kuma za mu yi aikin za mu hadu da likitoci daban-daabn da suka hada da na idanu da laka da na kashi. Likitan idon shi zai fara aiki don cire shi, kuma likitan laka shi zai gano yadda alakar halittun suke. Shi kuma likitan kashi shi zai yi aikin yadda za a cike ramin da za a samu yayin da aka cire idanun,” inji shi.
Dokta Hadi ya kara da cewa samuwar karin halitta ko ragi a wajen haihuwar jariri yana samuwa ne, a mafi yawan lokuta daga irin magunguna ko abinci ko rashin lafiya da uwar jaririn ta samu a lokacin goyon cikin jaririn.
“A lokuta da dama irin hakan takan faru a lokacin da aka samu mai juna biyu ta sha wasu magunguna barkatai, ko kuma ta rasa wani abinci maigina jiki. Ko kuma a lokacin da take goyon ciki ta yi fama da rashin lafiya da sauran abubuwa makamantan wannan.”