An haifi jariri da kai biyu da hannu hudu a Zariya
A ranar Alhamis din makon jiya ne wata mace ta haifi jariri da kai biyu da hannu hudu da kuma kafa biyu a Babban Asibitin Tunawa da Manjo Ibrahim D. Abdullahi da ke kofar Gidan Iya a karamar Hukumar Sabon Gari da ke Zariya a Jihar Kaduna.Wakilin Aminiya wanda ya je babban asibitin domin gane […]

A ranar Alhamis din makon jiya ne wata mace ta haifi jariri da kai biyu da hannu hudu da kuma kafa biyu a Babban Asibitin Tunawa da Manjo Ibrahim D. Abdullahi da ke kofar Gidan Iya a karamar Hukumar Sabon Gari da ke Zariya a Jihar Kaduna.
Wakilin Aminiya wanda ya je babban asibitin domin gane wa idonsa wannan abin al’ajabi, ya tattauna da mahaifiyar jaririn mai suna Husaibatu Hudu a kan yadda ta ji a lokacin da take dauke da cikin jaririn da kuma matakan da ta dauka don kula da cikin da kuma irin yadda ta ji lokacin da aka cire mata shi. “Sunana Husaibatu Hudu kuma shekaruna za su kai ashirin, kuma ni ’yar asalin kauyen Daga ne da ke karamar Hukumar kankara a Jihar Katsina ne. Aure ya kawo ni nan garin Zariya kuma yanzu muna zaune ne a gida Mai Lamba 187, wato gidan Musa Mai dankunne da ke Unguwar Marmara a Sabon Garin Zariya. Yanzu shekaruna biyu da yin aure, wannan cikin shi ne na farko ban taba haihuwa ba,” inji ta.
Ta kara da cewa: “A lokacin da Allah Ya ba ni wannan ciki na kasance ina ta rokon Allah Ya sa in haihu lafiya tunda ban taba haihuwa ba, don haka na fuskanci matsaloli daban-daban, kuma da cikin ya kai kamar wata uku sai na fara zuwa asibiti yin awo a Asibitin Kula da Lafiya a Matakin Farko da ke Tsohuwar Kwata, wato (Primary Healthcare) da ke Sabon Gari. A lokacin da nake zuwa sun sa na dauki hoto da kuma duk abin da mai ciki ya kamata ta yi, kuma suna ba ni kula sosai saboda ganin halin da nake ciki, don ina yawan koka musu cewa gefen damana ya yi nauyi da yawa. A kan haka sai suna shawartata da in rika hakuri kuma in daina yawan aikin wahala. Kuma idan na ji wani abu kis, to in yi maza in zo asibiti kada in kuskura in ce zan haihu a gida. Ashe sun san ko me nake dauke da shi kuma ba su taba fada min ba, domin gudun kada hankalina ya tashi.”
Malama Husaibatu ta ce a ranar Alhamis da ta ji alamun haihuwa sai ta tafi asibitin inda nan take suka tura ta Babban Asibitin da ke kusa da Gidan Iya a Sabon Garin, Zariya. Ta ce ba tare da bata lokaci ba likitan da suka tarar a wurin bayan ya gama duba ta, sai ya ce aiki za a yi mata na gaggawa. “To haka aka yi aikin ba tare da na san abin da na haifa ba sai bayan na farfado sannan na ga abin da Allah Ya ba ni. A lokacin kuma ya rigaya ya rasu,” inji ta.
Malama Husaibatu ta kara bayyana cewa, “Ganin halin da nake ciki da kuma abin da Allah Ya ba ni sai na yi maSa godiya kasancewar tunda Allah Ya ba ni cikin nan nake ta rokon Ya sa in haihu lafiya, kuma Allah Ya karbi addu’ata tunda na sauka lafiya duk da dai aiki aka yi min. Kuma ina kara samun sauki. Ina kara godiya ga Allah kuma ina godiya ga ma’aikatan asibitin musamman likitan da ya yi min aiki. Kuma Allah Ya ba ni wanda ba zan wahala da shi ba idan ya tashi ba ni haihuwa nan gaba.”
Matar da suke gida daya da Husaibatu mai suna Lubabatu Isa ta ce, a gaskiya Husaibatu ta wahala da cikin kwarai da gaske, domin shi ne na farko gare ta “Na san irin yanayin da ta shiga na wahala lokacin tana dauke da wannan ciki, don haka muna yi wa Allah godiya da ya raba ta da shi,” inji ta.
Aminiya ta tattauna da likitan da ya jagoranci yi wa Husaibatu aikin cire jaririn mai suna Dokta Abdullahi Sule, inda ya ce, “Asibitin kula da majinyata a matakin farko da ke Tsohuwar Kwata ne suka turo ta a ranar Alhamis, dama duk mata masu awo a wajensu idan lokacin haihuwa ya zo kuma haihuwar ta nemi ta zo da gardama sukan turo mana domin wannan asibitin yana gaba da nasu. Kuma duk muna karkashin Gwamnatin Jihar Kaduna ne. A lokacin da ta zo nan take na duba halin da take ciki, tare da hoton cikin, sai hoton ya nuna cewa jaririn bai zauna daidai ba, saboda kai na sama kafafuwa na kasa, sai na ga alamar ba za ta iya haihuwa da kanta ba, don haka muka dauki matakin yi mata aiki don mu cire dan kada ta wahala da yawa kuma ba za iya haihuwa da kanta ba kasancewar haihuwar fari ce. Allah Ya sa mun yi nasara domin mun ceto rayuwarta, shi kansa abin da aka haifa mun ciro shi da ransa daga baya kamar minti 30 ne muna kokarin ceto ransa Allah Ya yi masa rasuwa.”
Likitan ya ce jaririn ya sha bamban da jariran da aka saba haihuwa domin kansa biyu ne da hannaye hudu, “Don haka ya sha bamban da duk irin haihuwar da na saba gani ko na saba karba. A duk karatun da na yi da kuma labarin da na sha ji, ban taba haduwa ko karo da irin wannan ba, sai dai na taba jin labarin haihuwar irin wannan a kasar Indiya amma a nan Najeriya a gaskiya ban taba ji ko gani ba.”
Dokta Abdullahi Sule ya ce ya kamata idan mace za ta haihu a ce kai ne zai fara fitowa, to wannan kai biyu ne wanne ne zai fara fitowa, sannan ga shi suna sama don haka ba za ta iya haihuwa ba dole sai dai aiki.
Likitan ya ce kai biyu na jaririn sun hadu a kirji ne kuma duk abin da ke daya kan yana dayan kuma duk sun yi kuka, kafin su rasu.
Dokta Abdullahi Sule ya ce zai yi wuya a iya raba su, domin (kawunan) sun hadu ne a kirji abin numfashinsu wato huhunsu daya ne, kuma kayan cikinsu daya ne don haka zai yi wuya a rabu su.
Ya ce suna shirin tura su Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika ne domin su ke da kayayyakin da suka dace a kula da su da kyau, sai jaririn ya rasu.
Ya ce mahaifiyar jaririn tana ci gaba da jinya a asibitinsu kuma tana samun lafiya kuma nan ba da dadewa ba za su sallame ta.