An haifi jariri da sunan Allah rubuce a kunnuwansa

Wani abin al’ajabi ya bayyana a jikin wani jariri da aka haifa a ranar Juma’ar da ta gabata a Unguwar Sarankiyo da ke garin Gombe, inda kalmar ALLAHU ke rubuce a kunnuwansa biyu da haruffan Larabci. Mahaifin yaron mai suna Alhaji Hashimu Falalu, shi ya fara kula da lamarin a ranar Laraba a lokacin da […]

An haifi jariri da sunan Allah rubuce a kunnuwansa

Wani abin al’ajabi ya bayyana a jikin wani jariri da aka haifa a ranar Juma’ar da ta gabata a Unguwar Sarankiyo da ke garin Gombe, inda kalmar ALLAHU ke rubuce a kunnuwansa biyu da haruffan Larabci.

Mahaifin yaron mai suna Alhaji Hashimu Falalu, shi ya fara kula da lamarin a ranar Laraba a lokacin da ya dauki jaririn. Kamar yadda ya yi wa Aminiya bayani kafin ya ankarar da mahaifiyar jaririn mai suna Hafasah wadda ya aura a watan Disambar bara.

Ya bayyana cewa ya yi wa jaririn huduba a kunnuwansa a ranar da a ka haife shi ba tare ganin alamun rubutun ba sai a ranar. 

Binciken Aminiya ya gano cewa magidancin, wanda ya shafe shekara 15 da matarsa ta farko ba tare da haihuwa ba, sun rabu da ita gabanin ya auri ta yanzu, a sakamakon rashin amincewarta da aniyarsa na karin auren.

Ya ce an rada wa jaririn suna Muhammad Fadeel (Muhammad mai Falala) tun a ranar da a ka haife shi, sunan da iyayen suka zaba da nufin kara ga kakan jaririn.