An haifi jariri mai kai biyu da hannuwa uku

Wata mata mai suna Babita Ahirwar, mai shekara 21 ta haifi jariri mai kai biyu a manne a jiki da hannuwa uku a Indiya. Babita da mijinta Jaswant Singh sun ce, sun yi tunanin cewa za su samu tagwaye ne, sai dai bayan gwajin likita, ya nuna Babita tana iya haihuwar wanda ba tagwaye ba, […]

An haifi jariri mai kai biyu da hannuwa uku

Wata mata mai suna Babita Ahirwar, mai shekara 21 ta haifi jariri mai kai biyu a manne a jiki da hannuwa uku a Indiya.

Babita da mijinta Jaswant Singh sun ce, sun yi tunanin cewa za su samu tagwaye ne, sai dai bayan gwajin likita, ya nuna Babita tana iya haihuwar wanda ba tagwaye ba, kamar yadda suke tsammani kimanin mako 34 da samun junan biyu. Amma a wani fannin hoton likita kan cikin Babita ya nuna akwai yiwuwar a haifi jariri mai kai biyu.

Jaswant ya ce: “Matata ta sume bayan ta ga jaririn da ta haifa. Mun razana duk wanda ya kalli jaririn sai ya firgita saboda halittarsa. An sanar da mu cewa, za mu iya samun tagwaye kuma muna ta murnar maraba da samun tagwaye, amma sai ga shi an haifi jariri mai kai biyu.”

A cewar Jaswant, ‘Wannan dana ne zan ci gaba da rainonsa ta yadda aka yi halittarsa zan rike masa hannu. Jama’a da dama na ci gaba da fadin ra’ayoyinsu, a haka zan tafi da shi gida. Ba ni da kudin da za a yi masa tiyata, idan har yana da lafiya zan ci gaba da daukar nauyinsa.”

Wata kwararriyar likitar yara a Asibitin Indiya, Dokta Surendra Sonkar, ta ce za a dauki jaririn daga asibitin a kai shi wani asibitin kwararrun don yi masa tiyata.

Likitar ta ce, “Ana samun jariran da ake haihuwarsu da kai biyu a manne, amma muna amfani da shawarar kwararrun likitoci a garin Bhopal da Delhi.”

Akwai wani kwararren likita mai suna Dokta Pratibha Oswal, da kwananan ya yi irin wannan tiyata ga jaririn mai kai biyu. Kuma ya yi nasarar yin tiyatar ce bayan wata mata ta haifi danta na farko da yin aurentashekara daya da rabi. Tun kafin haihuwarta an yi hoton jaririn yana mahaifa an sanar da ita cewa, za ta haifi mai kai biyu bayan mako 35 da samun juna biyu.