An haifi jaririya da alamun sunan Allah a hannunta
A ranar Lahadin da ta gabata ne a unguwar Kan Tudun Madabo, karamar Hukumar Dala, Jihar Kano aka haifi wata jariiya tare da alamun sunan Allah a ’yatsun hannunta guda biyu.Sai dai ba kamar yadda aka saba samun rubutu a jikin yaran da aka haifa da irin wannan baiwar ba, ita wannan yarinyar tata baiwar […]

A ranar Lahadin da ta gabata ne a unguwar Kan Tudun Madabo, karamar Hukumar Dala, Jihar Kano aka haifi wata jariiya tare da alamun sunan Allah a ’yatsun hannunta guda biyu.
Sai dai ba kamar yadda aka saba samun rubutu a jikin yaran da aka haifa da irin wannan baiwar ba, ita wannan yarinyar tata baiwar daban take, domin halittar ’yan yatsun hannunta ne ke bayyana sunan Allah sakamakon harhadewa da juna da suka yi. A hannunta na hagu siffar sunan Allahu da Larabci ne aka yi. Haka kuma a hannunta na hagu, siffar sunan Annabi Muhammad (SAW) ne aka yi.
Da take yi wa Aminiya karin haske game da yadda ta haifi jaririyar, mahaifyar jaririyar mai suna Amina Murtala, wace shekarunta ba su wuce 30 ba, ta bayyana cewa a lokacin da ta haifi jaririyar ta zo kanta a sunkuye kamar mai yin sujjada, hannayenta rungume a kan kirjinta. “Bayan na haife ta sai na dago ta sai na lura da yanayin halittarta inda na ga ashe kafarta guda daya ce, haka kuma ’yan yatsun hannayenta a mammane da juna suke.” Inji ta.
Malama Amina ta kara da cewa duk da cewa wannan haihuwar ita ce karo na bakwai a wurinta, ta zo mata da bamabanci ba kamar sauran haife-haifen da ta yi a baya ba.
Sai dai saboda irin dimbin jam’ar da ke tururuwa zuwa gidan don ganin jaririyar, tuni Hukumar Hisba ta karamar Hukumar Dala ta dauke mai jegon ta mayar da ita karkashin kulawarta kamar yadda Mataimakin Kwamnadan Hisba na yankin, Malam Abubakar M. Salihu ya shaida wa Aminiya.
“Bayan mun sami labarin haihuwar wanann jaririya da irin cikar da ake yi a gidan wajen ganin ta sai na shawarci Kwamandana a kan yadda ya kamata mu bullo wa al’amarin. Nan ne ya umarce ni da na tura jami’anmu wurin domin su yi wa jama’a wa’azi. Da farko mun fara tura jami’anmu mutum takwas mata da maza amma daga bisani bisa irin rahotannin cikowar da ake yi a wurin ya sa da kaina na je na gane wa idanuna halin da ake ciki. Jama’a kai ka ce a filin Idi, wanda hakan barazana ce ga lafiyar jama’a domin zai iya sanyawa a rasa rai ko kuma a samu raunuka ko kuma sace-sace. A gefe guda kuma mutanen gida har suna karbar dan wani abu a hannun mutanen da suke son ganin yarinyar. Bayan na dawo muna tattauna matakin da za mu dauka sai ga dattawan unguwar sun kawo mana korafi cewa su fa a unguwar an dame su, ba su da ikon su shiga gidajensu sai dai su kulle kofofinsu. Ita kanta maijegon saboda yawan jama’a ba ta samun kulawar da ta kamata, hakan ya sa ta yi gudun hijira zuwa ofishinmu, inda a nan muka kai ta asibiti aka auna jininta har ya yi muguwar haurawa sama, ga kuma yunwa da take damunta. A nan Hisba ta saya mata magunguna tare da taimakon asibitin da ke Gwammmaja ga shi an samu ta dawo hayyacinta.” Inji shi.
Malam Ibrahim Mu’azzam na bangaren da’awah a Hukumar Hisba, ya nemi jama’a da su dauki wannan al’amari a matsayin ayar Allah wacce yake bayyanar da ita a duk lokacin da ya so. Ya shawarci jama’a da su kara sanin Allah tare da kadaita Shi, duk irin lokacin da abubuwa makamanta wadanan suka faru jama’a su rika giramama sha’anin Allah.
A ziyarar da Aminiya ta kai ofishin Hisba na Dala, ta tarar da jaririyar wacce aka rada wa suna Sa’adatu cike da koshin lafiya ita ma Maijego Amina ta fara farfadowa.