An haifi jaririya dauke da cikin ’yan biyu a kasar Sin

An haifi jaririya mai dauke da cikin ’yan biyu a kasar Sin, kuma har yanzu masana ba su gano hakikanin yadda wannan matsala ta auku ba. Mahaifiyar wannan jaririya da ke kasar Sin ta haifi ’yarta, wadda daga bisani aka gano tana dauke da cikin ’yan biyu, al’amarin da masana a fannin likitanci suka tabbatar […]

An haifi jaririya dauke da cikin ’yan biyu a kasar Sin
An haifi jaririya dauke da cikin ’yan biyu a kasar Sin

An haifi jaririya mai dauke da cikin ’yan biyu a kasar Sin, kuma har yanzu masana ba su gano hakikanin yadda wannan matsala ta auku ba. Mahaifiyar wannan jaririya da ke kasar Sin ta haifi ’yarta, wadda daga bisani aka gano tana dauke da cikin ’yan biyu, al’amarin da masana a fannin likitanci suka tabbatar da aukuwarsa a makon da ya wuce.
Likitocin sun gano wannan jaririya ne bayan da aka haifeta a Asibitin Sarauniya Elizabeth, inda take dauke da wani kumburi a cikinta. Daga bisani suka gano cewa, ashe ’yan biyu ne a cikinta. “kuma a kalla girmansu ya kai makonni 10,” a cewar likitocin.
Likitoci sun yi wa wannan jaririya tiyata, inda suka cire ’yan tayin da girmansu bai wuce na ’yan makonni biyu ba.
Kowane daya daga cikin ’yan tayi yana da hannaye da kafafuwa da hakarkari da mafitsara da laka da hanji da dubura da jiyoyin da suka hade kwakwalwa, sannan duk an linke su a cikin mahaifa. Nauyin wannan jaririya ya kai kilo hudu.
Irin wannan yanayi da likitoci suka yi wa lakabi da ’yan tayi a cikin ’yan tayiwa, wato a Turancinsu, ana kiransa da “fetus-in-fetus,” tuni aka wallafa aukuwa al’amari a wata mujallar nazarin likitanci ta Hong Kong Medical Journal. A cewar mazanarta da suka yi rubutu a wannan mujalla, ba a cika samun irin wannan yanayi ba, domin akalla ana samun daya cikin dubu 500. “A daukacin fadin duniya irin wannan yanayi 200 aka taba samu,” kamar yadda mujallar ta ruwaito.