An haifi jaririya mai kafa hudu da al’aura biyu
Al’ummar Sabon Garin Makiyawa da ke garin Magamar Jibiya sun ga abin mamaki a makon jiya sakamakon haihuwar wata yarinya mai dauke da kafafu hudu da al’aura biyu da hannuwa biyu. Jaririyar an haife ta da kafafu hudu, cibiya biyu, mazakunta biyu, na mace da ta namiji a can gefenta na dama. A wannan bangaren […]

Al’ummar Sabon Garin Makiyawa da ke garin Magamar Jibiya sun ga abin mamaki a makon jiya sakamakon haihuwar wata yarinya mai dauke da kafafu hudu da al’aura biyu da hannuwa biyu.
Jaririyar an haife ta da kafafu hudu, cibiya biyu, mazakunta biyu, na mace da ta namiji a can gefenta na dama. A wannan bangaren ne aka fito da kafafu biyu wadda daya ta fi daya, sai kuma mazakuntar namiji karama da kuma cibiya da wani dan kullutu a sashen dai na dama. Sai kuma halittar mace wadda ita ce tafi rinjaye da kafafu biyu wadanda suke a daidaice kamar yadda aka saba gani da kuma hannuwanta biyu.
Mahaifiyar yarinyar Malama Zainab Hassan mai kimanin shekara 20 wadda ta ki yarda a dauki hotonta, ta ce, wannan ita ce haihuwarta ta biyu a cikin shekara hudu da yi mata aure. Kuma kamar yadda ba ta samu matsala ba a haihuwata ta farko duk da cewa a asibiti ta yi, haka ma wannan ba ta samu wata matsala ba.
Zainab ta ce da farko ta ji alamun haihuwa ta zo mata da yammacin daren da za ta haihu, kuma sun je asibiti ita da abokiyar zamanta, amma sai suka dawo gida bayan ta samu sauki. Ta ce sun dawo gida ne saboda nakudar ba ta yi mata tsanani ba, kuma sun dawo ne ba tare da sun yi wa kowa magana a asibitin Shema da ke Magamar Jibiya inda take zuwa awon ciki.
Zainab ta ce, “Sai cikin dare ne na ji haihuwar ta zo gadan-gadan, amma kafin mijina ya dawo daga neman mota don a dauke ni zuwa asibiti, sai ya shigo ya tarar har na haihu.” Game da ganin wannan halitta da Allah Ya ba ta da ba a saba ganin irinta ba, Zainab ta ce, “In baya ga gode wa Allah babu abin da na yi. Ni dai ce na haifo ta, daga jikina ta fito, to tsoro ko fargabar me zan yi? Kuma in ka debe irin laulayin ciki na farko-farkonsa har zowa lokacin da na haihu ban sha wata wahala ba. Ai ga shi ma a gida na haihu kuma lafiya.”
Zainab ta ce, ko a cikin danginta ba ta taba jin an yi irin wannan haihuwa wadda za a ce abin da aka haifar ya zo da wata siffa ko wasu alamu wadanda ba a taba gani ba.
Shi kuwa mijinta kuma mahaifin jaririyar, Malam Hassan Ibrahim mai kimanin shekara 32, ya ce, Zainab ce matarsa ta biyu kuma kimanin shekara hudu ke nan da ya aure ta budurwa, akwai dansu na farko mai suna Fahad mai kimanin shekara biyu da rabi. “Ganin wannan baiwa da Allah Ya ba ni ban guje ta ko kin son ta ko kuma jin wani tsoro ba, saboda na san ikon Allah Ya wuce haka. Wadansu ma ba su zuwa duniyar su yi numfashi balle har a gan su, yanzu kuwa da nake magana da ku kwanan wannan yarinya hudu da haihuwa kuma babu alamun wani ciwo na daban game da ita in baya ga wannan lalura da Allah Ya kaddare ta da ita. Kuma babban farin cikina shi ne da aka ce za a iya cire mata wannan bangare na mutum (namiji) da aka haife ta da shi kuma ta rayu cikin ikon Allah.”
Sai dai kuma kamar yadda ya ce, kasancewarsa mai karamin karfi da ke sayar da kayan dinkin keke, ba ya da halin da zai dauki nauyin yi wa jaririyar aiki don haka ne ya je karamar Hukumar Jibiya neman taimako saboda an tura su zuwa Asibitin Malam Aminu Kano don yin aikin.
Malam Hassan ya ce, bai taba jin labarin irin wannan haihuwar daga bangarensa ba, sai dai ya kara samun natsuwa tare da imani bisa ga ikon Allah wanda babu abin da yake gagararSa.
Har zuwan Aminiya uwar da jaririyar suna cikin koshin lafiya, kuma tuni karamar Hukumar Jibiya ta hada su da Daraktan Sashen Lafiya na karamar Hukumar domin yin abin da ya kamata tunda an tura su zuwa asibitin Malam Aminu Kano domin yin gwaje-gwaje tare da sanin irin yawan kudin da aikin tiyatar zai ci.