An haifi jaririya mara hanci

An haifi jaririya ‘yar wata 17 babu hanci a yankin Ireland da ke karkashin Birtaniya, a wani gari da ake kira County Derry. Jaririyar mai suna Tessa Ebans, wadda ke da wannan matsala da a likitanci ake yi wa lakabi da arhinia, an tabbatar da cewa ba ta da hanci.Mahaifiyar Tessa, Grainne Ebans, ta ce […]

An haifi jaririya mara hanci
An haifi jaririya mara hanci

An haifi jaririya ‘yar wata 17 babu hanci a yankin Ireland da ke karkashin Birtaniya, a wani gari da ake kira County Derry. Jaririyar mai suna Tessa Ebans, wadda ke da wannan matsala da a likitanci ake yi wa lakabi da arhinia, an tabbatar da cewa ba ta da hanci.
Mahaifiyar Tessa, Grainne Ebans, ta ce ba ta fahimci halin da Tessa ke ciki ba, har sai da ta shaki numfashin farko.
“Na yi matukar jin dadin haihuwa a karo na farko ba tare da matsala ba, amma da na ga fuskarta sai na fahimci akwai amtsala. Na  girgiza matuka. Malamar asibiti na yanke mahaifa sai kawai ta tafi da jaririyar kafin ma in ce wani abu. Sai na yi ta jin karar kararrawa, don haka na cika da tsoro,” injita.
An sanar da iyayen wannan jaririyar ne wannan matsalar da ’yarsu ke fama d aita, bayan da ta cika makonni 20 a duniya.