An haifi karya mai kafa takwas a Austeriliya
A ranar Larabar makon jiya aka haifi wata karya mai kafa takwas da kuma bindi biyu a wani tsibiri mai suna, Tonga da ke nahiyar Austeriliya, kamar yadda jaridar Daily Mirror ta bayyana.. Karyar mai launin fari da baki ta jefa al’ummar garin cikin dimuwa don kamar yadda wani mazaunin garin bukitangitau Maloni ya bayyana […]
A ranar Larabar makon jiya aka haifi wata karya mai kafa takwas da kuma bindi biyu a wani tsibiri mai suna, Tonga da ke nahiyar Austeriliya, kamar yadda jaridar Daily Mirror ta bayyana..
Karyar mai launin fari da baki ta jefa al’ummar garin cikin dimuwa don kamar yadda wani mazaunin garin bukitangitau Maloni ya bayyana ba su taba ganin irin wannan abin al’ajabin ba.
Kodayake, an ruwaito cewa jim kadan bayan haihuwar karyar ta yi yunkurin fara tafiya, amma sai hakan ya faskara. Kuma sa’o’i kadan bayan wannan ne, sai ta ce ga garinku nan.
Wata ma’aikaciya a wani asibitin dabbobi ta ce irin wadannan dabbobin ba su cika rayuwa ba. Kuma ta ce ba ta taba ganin irin wannan a baya. Amma ta ce hakan na faruwa ne sakamakon karancin abinci da tawayar wasu kwayoyin halitta lokacin kenkesarsu.