An haifi mannannun tagwaye da kafa uku da hanta daya a Abuja
Wata matar aure mai suna Patient Elisha, ’yar shekara 28 da ke zaune a Garin Mpape a karamar hukumar Bwari da ke yankin Birnin Tarayya Abuja, ta bayyana mamakinta a game da tagwaye da ta haifa ta hanyar fida wadda a ka haifesu a hade. Jariran biyu wadanda al’aurarsu ke dauke da yanayi biyu da […]

Wata matar aure mai suna Patient Elisha, ’yar shekara 28 da ke zaune a Garin Mpape a karamar hukumar Bwari da ke yankin Birnin Tarayya Abuja, ta bayyana mamakinta a game da tagwaye da ta haifa ta hanyar fida wadda a ka haifesu a hade. Jariran biyu wadanda al’aurarsu ke dauke da yanayi biyu da likitoci suka kasa tantace mazantaka ko matantaka ce, na dauke da kai biyu da hannaye hudu sai kuma kafafu uku a rarrabe.
Lamarin wanda ya faru a ranar Talata ta makon jiya, ya biyo bayan tsawon nakuda ne da matar ta fuskanta, daga nan ne kuma ganin karfin jikinta na ci gaba da raguwa sai likitoci a asibitin Luna Hospital and Maternity da ke Kado a yankin Birnin Tarayya Abuja, inda a ka garzaya da ita, su ka yanke shawarar yi mata aiki, a nan ne kuma a ka fito da tagwayen biyu a hade.
Da ta ke zantawa da wakilinmu a asibitin inda ta ke murmurewa, Madam Patient Elisha wadda ‘yar asalin jihar Akwa Ibom ce, ta ce, ko da ya ke tun ta na da wata shida da cikin, a ka sanar da ita cewa tagwaye ne take dauke da su, ba ta taba tsammani ko jin wasu alamu a game da cikin ba, wanda ya bambanta da na baya da ta haifa har sau biyu, in ban da karin nauyi. Ta ce ba a sanar da ita irin abin da ta haifa ba, sai bayan kwana biyu da haihuwa ta ji wa su daga cikin masu kula da ita suna magana a kan al’amarin cikin harshen Hausa, a nan ne ta dage a kan sai taga ’ya’yan. A lokacin ne kuma a ka sanar da ita inda suke, wato babban Asibitin kasa na Abuja.
A ganawarta da Aminiya, babban likitan asibitin Dokta bictor Akpan ya ce an kai yaran ne asibitin na kasa, don nazari a kan yiwuwar yi masu aiki, sai dai bayanin da ya samu daga asibitin shi ne, su ma sun yanke shawarar aikewa da jariran zuwa kasar Jamus . Dokta Akpan wanda ya bayyana tababarsa ga yiwuwar ci gaba da rayuwar yaran a hade ko arabe, ya ce matsala irin ta su wadda ta shafi hadewar zuciya, da koda, da kuma huhu, yana da sarkakiya, kuma ba ya jin a kwai wani Asibiti a duniyan nan wanda zai samu nasara a kan wannan.
A game da ko a za a iya sadaukar da guda don ganin guda ya tsira, babban likitan ya ce, “ba na son tsawaita magana kuma ba na so na yanke hukunci a kan wannan. Sai dai ya ce tuni uwar ta samu lafiya, amma kasancewar iyalan na fama da matsalar rashin abun hannu, sun yanke shawarar ci gaba da kasancewarta a karkashin kulawar asibitin sai bayan sun biya kudin da asibitin ya yanka musu tukuna. Ita ma uwar jariran a yayin ganawarta da wakilinmu, ta bayyana rokonta ga gwamnatoci, da kungiyoyin jinkai, da kuma daidaikun jama’a da su kawo mu su dauki. kokarin jin ta bakin mahaifin tagwayen, wanda ke sana’ar tireda a Garin Mpape bai yi wu ba. kasancewar ba ya wajen matarsa haka nan ba kuma same shi a babban Asibitin kasa ba, a lokacin da wakilinmu ya garzaya can.