An haifi maraka da kai biyu

Wata saniya ta haifi maraka mai kai biyu a wani gidan gona da ake kiwon shanu a Amurka. Wata mata mai Heather Herman mai shekara 30 ce ta gano wannan ’yar saniyar ce kwance a gidan gonarsu da ke yankin Montana a kasar Sifaniya. Misis Herman, ta ce ta yi mamakin abin da ta gani, […]

An haifi maraka da kai biyu

Wata saniya ta haifi maraka mai kai biyu a wani gidan gona da ake kiwon shanu a Amurka.

Wata mata mai Heather Herman mai shekara 30 ce ta gano wannan ’yar saniyar ce kwance a gidan gonarsu da ke yankin Montana a kasar Sifaniya.

Misis Herman, ta ce ta yi mamakin abin da ta gani, a maimakon ta ga ’yar saniya mai halittar saniya sai ga ’yar saniya da kai biyu lokacin da taje duba dabbobin da suke kiwo a garken su.

Ta samu saniyar ne kwance daga nesa, sai daga bisani ta fahimci cewa, akwai alamar wannan ’yar saniyar nada larura. Hakan yasa ta fahimci cewa, akwai abin da ke damun wannan ’yar saniyar, sai ta ce ba ta son ta rasa daya daga cikin shanun ako wane hali. Wannan halittar ’yar saniyar yasa na gaza kallon siffar halittar saniyar.

Misis Herman, ta yi matukar mamakin ganin saniya da ta haifi mai kai biyu da kanta ba tare da neman agajin kowa ba, wanda hakan abu ne mai sauki ta mutu. Sai ga shi bayan haihuwar tana da koshin lafiya, haihuwar ba ta shafi lafiyarta ba. Abin bacin ran shi ne ’yar saniyar da aka haifa ta mutu bayan wani lokaci kadan.

Misis Herman, ta kara da cewa, wannan ba shi ne na farko da saniya ta taba haihuwar mai kai biyu ba, a wannan garken shanun, amma hakan ya faru ne kafin in fara lura da garken shanun. A lokacin da nake tattaunawa da kakata ta fada min cewa, ”Na taba ganin saniyar da ta haifi ’ya mai kai biyu har sau biyu, wand aba kowa bane ya taba ganin irin wannan halittar“.

Ba kowane lokacin ne akan samu dabba jinsin saniya ta haifi ’ya mai kai biyu ba.