An haifi maraki mai kai biyu a Amurka

A ranar Litinin da ta gabata ne a Jihar Florida ta kasar Amurka wani makiyayi ya tsinci kansa cikin mamaki bayan da wata saniyarsa ta haifi wani maraki mai kai guda biyu. Sai dai masana dabbobi sun ce wannan wata lalura ce da ake samu sau daya a kowace haihuwa miliyan 400. Kuma suna ganin […]

An haifi maraki mai kai biyu a Amurka
An haifi maraki mai kai biyu a Amurka

A ranar Litinin da ta gabata ne a Jihar Florida ta kasar Amurka wani makiyayi ya tsinci kansa cikin mamaki bayan da wata saniyarsa ta haifi wani maraki mai kai guda biyu.

Sai dai masana dabbobi sun ce wannan wata lalura ce da ake samu sau daya a kowace haihuwa miliyan 400. Kuma suna ganin da wuya wannan dan maraki da aka rada wa suna Annabel ya yi rayuwa mai tsawo. Amma duk da haka makiyayin da ya mallake shi ya ce hakan ba zai hana shi kaunarsa kuma ya sha alwashin kulawa da shi har karshen rayuwarsa.
Kodayake, masana sun ce Annabel yana fama da wata lalura ce da ake kira Polycephaly, wadda take faruwa sakamakon baruwar dan tayi gida biyu, amma ba tare da haifar da cikakkun ’yan tagwaye ba.