An haifi maraki mai kai biyu da jikin alade
Wata saniya ta haifi maraki mai kai biyu da jikin na alade a kasar Rasha.
Wata saniya ta haifi maraki mai kai biyu da jiki irin na alade a kasar Rasha.
Wannan lamari ya faru ne a kauyen Matkechik, Khakassia na kasar Russia bayan mai saniyar ya shaida wa jama’a abin da ya faru.
Mai saniyar ya ce wannan shi ne karo na farko da saniyar ta haihu kuma sai gashi ta haifi maraki mai kai biyu da jiki irin na alade ba irin na shanu ba.
Marakin ya mutu ne bayan an haife shi, ita ma mahaifiyarsa ta rasu bayansa duk a lokaci guda.
Hoton da aka dauka bayan mutuwar marakin ya nuna shi da kai biyu irin na shanu tare da idanu a like sannan kuma da harshe a kowane kai, jikinsa kuma irin na alade.
A shekarar da ta gabata ma an samu marakin da aka haifa da kai biyu a kasar China, kuma ya rayu na dan lokaci.