An haifi wani dan maraki da fuskar mutum a kasar Ajantina

An haifi wani dan maraki da fuskar mutum duk da cewa ya mutu awanni kadan da haihuwarsa a kasar Ajentina, sai dai an yi ta watsa hotunan bidiyonsa a Intanet. Haihuwar dan marakin da fuskar mutum ya tsorata manoman da suka ganshi kafin ya mutu. A cikin wani faifan bidiyo da mazauna kauyen Billa Ana […]

An haifi wani dan maraki da fuskar mutum a kasar Ajantina

An haifi wani dan maraki da fuskar mutum duk da cewa ya mutu awanni kadan da haihuwarsa a kasar Ajentina, sai dai an yi ta watsa hotunan bidiyonsa a Intanet. Haihuwar dan marakin da fuskar mutum ya tsorata manoman da suka ganshi kafin ya mutu.

A cikin wani faifan bidiyo da mazauna kauyen Billa Ana na kasar Ajentina suka nada wanda daga bisani ya shiga shafin YouTube an ga dan marakin da karamin hanci da karamin baki yana kokari rike faffadan kansa. Sai dai kamar yadda rahoton ya ce marakin ya mutu ’yan awoyi kadan bayan haihuwarsa.

Wani masanin halitta mai suna Nicolas Magnago ya fada wa kafar labaran dabbobi cewa wannan dabbar ta samu matsala ce a yayin da halittarta take kammala a cikin uwarta. “Akwai yiwuwar samun wani sauyi wanda ba safai ake samunsa ba a cikin kwayoyin halittar wannan saniya. Wani sauyi ne na halitta ya auku wanda ya jirkita kwayoyin halittarsa, kuma zai iya samuwa daga wasu abubuwa da suka faru ko dai a zahiri ko saboda tasirin wasu sinadarai,” inji shi.

Haihuwar marakin ta zo ne shekara biyu bayan haihuwar wani maraki mai kai biyu da ido hudu da baki biyu a Arewacin Jihar Himachal Pradesh ta kasar Indiya, wanda aka ga mai dabbar yana duba ta a cikin wani faifan bidiyo. Lamarin ya faru ne a wani kauye mai suna Shimla.

Bayan haka an sake samun haihuwar irin wannan dabba a garin Rajasthan na Gundumar Udaipur a kasar ta Indiya wanda shi ma ya dauki hankalin manema labarai a farkon bara.

Abin da ya bambanta maraki na farkon da na biyu shi ne wurin da idanunsu suke, domin marakin da aka haifa a Udaipur idanuwansa suna kusa da juna daf-da-daf yayin da na Shimla idanuwansa suna gefe da gefe ne.